Kotun tafi – da – gidanka ta kama mutane 111 bisa laifin karya dokar tsaftar muhalli a Kano

289

Kimanin mutane 111 ne a ka kama da laifin karya dokar tsaftar muhalli ta wata-wata a Jihar Kano. Kamar yadda kwamishinan Muhalli Dakta Kabiru Getso ya baiyana a lokacin da ya ke zagayen tsaftar mahalli da a ke yi a duk ranar Asabar ɗin ƙarshen wata a jihar.

Ya ce a yayin gudanar da zagaye don tabbatar da bin dokar, jami’an ma’aikatar muhalli ta Kano a ƙarƙashin jagorancin Getso da kuma jami’an sun samu mutane 111 waɗanda suka karya dokar.

Kwamishinan ya ƙara da cewa an tarar masu laifin N123,200 dukkan su kotun tafi-da-gidanka.

Dakta Kabiru Getso ya bayyana cewa a shirye gwamnatin jihar Kano ta ke ta cigaba da bayar da kulawa ga al’umma domin kula da muhallan su.

Ya ƙara da cewa gwamnatin Abdullahi Ganduje ta himmatu wajen tsaftace muhalli domin kawar da duk wata cuta da take yaɗuwa a cikin al’umma.

Kwamishinan muhallin ya ƙara da cewa an samar da wannan doka ta gyara muhalli na karshen wata ne domin al’umma su zauna a gidajen su don kawar da duk wata ƙazanta da ta ke tattara a muhallan al’umma.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan