Ko Me Ya Sa Shugaban Twitter Zai Ajiye Muƙaminsa?

88

Jack Dorse, Shugaban Kamfanin Twitter zai ajiye muƙaminsa a shekarar 2022.

Parag Agrawal, jami’in kula da fasaha na Twitter ne zai maye gurbin Mista Dorsey.

Mista Dorsey zai ci gaba da riƙe muƙamin har zuwa 2022, lokacin da wa’adinsa zai cika, kamar yadda Twitter ya sanar.

“Na yanke shawarar barin Twitter saboda na yi imanin kamfanin a shirye yake ya ci gaba daga waɗanda suka samar da shi. Na amince da Parag sosai a matsayin Shugaban Twitter. Aikin da ya yi a shekarau 10 da suka gabata sun sauya abubuwa sosai. Na ji daɗin ƙwarewarsa ƙwarai da gaske. Lokaci ya yi da ya kamata ya ja ragama”, in ji Mista.

Ya kuma rubuta wa ma’aikatansa saƙon email na ƙarshe a matsayin Shugaban Twitter, inda ya ce: “Abin baƙin ciki ne… kuma abin farin ciki”.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan