Idan Ajali Ya Yi Kira: Jirgin ruwa ɗauke da ɗalibai 47 ya nutse a Bagwai da ke jihar Kano

271

Wasu rahotanni daga garin Badau da ke yankin ƙaramar hukumar Bagwai a jihar Kano sun bayyana cewa wani kwale -kwale da ya ɗebo dalibai maza da mata daga garin Badau zuwa Bagwai domin halartar Maulidi ya yi haɗari a cikin ruwa inda ya nutse da ɗalibai fiye da 47.

Tun da farko shafin Jarida Radio da ke Facebook ne ya wallafa labarin, inda ya rawaito cewa kwale – kwalen ya nutse da ɗaliban ne akan hanyarsu ta zuwa gurin Maulidi.

Haka kuma kawo lokacin haɗa wannan rahoton rahotanni daga ƙaramar hukumar ta Ɓagwai sun nuna cewa an samu nasarar ceto ɗalibai 4 daga cikin 47 yayin da aka tsamo gawarwakin mutane goma (10).

Sai dai har zuwa yanzu ana cigaba da neman sauran ɗaliban da kwale – kwalen ya nutsa da su a cikin ruwan.

Wakilin Labarai24 ya tuntuɓi da kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa sai dai bai same shi ba.

Wannan shi ne karo na 2 da irin wannan nitsewar kwale – kwalen ya faru a ƙaramar hukumar Bagwai din da ke jihar kano.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan