CITAD ta horas da matan da za su dinga koyar da ɗalibai mata hanyoyin kare kai daga cin zarafi

228

A ƙoƙarin ta na ganin ta kawo karshen cin zarafin mata a jihar Kano, cibiyar bunƙasa fasahar sadarwa da cigaban al’umma wato CITAD, ta horas da mata guda 21 da za su dinga zuwa wasu daga cikin makarantun ƴan mata da ke jihar domin koyar da ɗalibai dabarun kare kai daga cin zarafin.


Taron wanda ya gudana a ofishin cibiyar da ke Kano, ya samu halarcin kwararrun mata da su ka yi fice a harkokin yaƙi da cin zarafi tare kuma bayar da shawarwari domin kaucewa faɗawa hannun masu wannan mummunar ɗabi’ar.

Da ya ke jawabi a lokacin buɗe taron horarwa babban jami’i mai kula da harkokin kungiyoyin’ na cibiyar CITAD din Malam Haruna Adamu Hadejia kira ya yi ga matan da su ka samu horon da su mayar da hankali wajen ganin sun koyar da ɗaliban abin da ya kamata.

Malam Haruna Hadejia ya ce la’akari da yadda ake ƙara samun ƙaruwar cin zarafin mata a birni da ƙauye ya sanya CITAD ta tashi tsaye wajen wayar da kan mutane akan illar da ke tattare da hakan.

Malam Haruna Adamu Hadejia

A nata ɓangaren Zainab Aminu, wadda ita ce babbar jami’a mai kula da al’amuran mata a cibiyar ta CITAD ta ce sun zaɓi makarantun ƴan mata goma sha ɗaya a jihar Kano, inda za su tura matan da su ka samu horon domin koyar da ɗaliban.

Haka kuma Zainab ɗin ta bayyana cewa cibiyar ta CITAD ta samar dakunan kwamfuta wato ICT Centre a makarantun sakandaren ƴan mata guda biyu da za su zama wata cibiyar aikewa da sakon duk wani rahoton cin zarafi da ya faru.

Hakazalika jami’ar ta bayyana cewa baya ga wannan kuma ana sa ran za a dinga koyar da matan sana’o’in dogaro da kai domin damawa da su a harkar cigaban kasuwanci da sauran al’amuran rayuwa.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan