Mata Iyayen Giji: An yi gangamin yaƙi da cin zarafin mata a Kano

469

A yau Asabar Mata da Matasa da kuma masu fafutukar kare jinsi da ƙungiyoyi masu zaman kansu da kuma ɗaiɗaikun jama’a su ka yi wani gangami tare da yin tattaki a birnin Kano, domin nuna ƙyama tare da wayar da kan mutane akan illar da ke tattare zarafin mata tare da keta musu haddi.

Gangamin wanda aka fara shi daga sakatariyar Audu Bako zuwa kan titin fadar gwamnatin Kano, ɗaruruwan mata ne su ka fito ɗauke da kwalaye masu rubuce-rubuce akan illar da ke tattare da cin zarafin mata.

A lokacin gangamin masu fafutukar kare hakkin bil’adama da hana cin zarafin mata sun nuna damuwa game da yadda ake ƙara samun ƙaruwar cin zarafin mata musamman wanda ya ke da nasaba da fyaɗe.

Wani ɓangare na gangamin

Haka kuma sun bayyana damuwa game da matsalar fyade da kuma yadda ake sace mata da kuma ƴan mata musamman a yankin arewacin Najeriya.

Ana dai samun ƙaruwar matan da ake cin zarafinsu ta hanyar lalata da su da kuma wasu nau’oin cin zarafi a sassa daban-daban na duniya. Domin kusan a kowacce rana dai sai an samu labarin cewa an yi wa wata ko wani fyaɗe a Najeriya.

Ƙungiyoyi musamman masu fafutikar kare hakkin mata da ƙananan yara, na ta yin kumaji da kuma nuna damuwa kan matsalar ta fyade – matsalar da wasu ke cewa ta zama annoba a cikin al’ummar ƙasar nan.

Turawa Abokai

1 Sako

  1. Hakika munji dadi yadda aka samu wannan tattaki muna kara kira da al umma dasu dauki wannan tattaki a matsayin wata hanya da zasu gyara duk wani cin zarafi da akewa mata domin mata sune iyayenmu kuma sune matayenmu don haka muna kira da gwammanati data yi wata doka kan cin zarabin mata da kananan yara kamar yadda gwammanatin kasa ta zartar.

    Wani mawakai yana cewa “yan uwa kubar rena mata mata iyayenmune suu” Allah yakawo mana zaman lafiya mai dorewa awannan kasa da wannan jaha tamu.

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan