Rikicin APC A Kano: Yadda zaman sulhu ya kasance fadar gwamnatin Kano

  3927

  Mai Mala Buni, gwamnan jihar Yobe kuma shugaban kwamitin riko sannan shugaban kwamitin shirya taron fitar da shugabannin jam’iyyar APC na kasa shi ne ya kafa kwamitin sasanci da daidaito a duk fadin Najeriya, saboda warware matsaloli na korafe-korafe daga ‘ya’yan APC.

  Ranar 14 ga watan Satumba 2021 Mai Mala ya rantsar da kwamitin mutum tara domin su yi masa aikin sasanta masu kuka da korafi. Mutanen da aka baiwa wannan aikin sune: Sanata Abdullahi Adamu, tsohon gwamnan jihar Nassarawa, a matsayin shugaba. ‘ ‘ sauran ‘yan kwamitin sune; Barista Ali Sa’adu Birnin Kudu tsohon gwamnan jihar Jigawa da Alhaji Sulaiman Argungu, tsohon mataimakin gwamnan jihar Kebbi da tsohon gwamnan Enugu Sullivan Chime da tsohon kakakin majalisar tarayya Rt. Yakubu Dogara da tsohon gwamnan Binuwai George Akume da tsohuwar mataimakiyar gwamnan Lagos Oluranti Adebule, da kwamishinan lafiya na jihar Cross River Beta Edu sai Moses Adeyemi a matsayin sakatare.

  Gwamna Abdullahi Umar Ganduje

  Ranar 13 ga watan Oktoba 2021 Sanatoci guda uku na Kano karkashin jagorancin Sanata Mallam Ibrahim Shekarau da Sanata Barau I Jibrin da Sanata Kabiru Ibrahim Gaya da ‘yan majalisar tarayya guda hudu, Hon. Tijjani Abdulkadir Jobe da Hon. Nasir Abduwa Gabasawa da Hon. Haruna Isa Dederi da Hon. Sha’aban Ibrahim Sharada suka hadu a gidan Sardaunan Kano na Abuja suka tattauna yadda za su gabatar da kokensu ga uwar jam’iyyar APC ta kasa a rubuce. Da asubahin fari Sanata Kabiru Ibrahim Gaya ya sanar da ficewarsa daga wannan shiri da tsari.

  Sanata Malam Ibrahim Shekarau

  Ranar 14 ga watan Oktoba 2021 bayan sallar Juma’a wadannan shugabannin tare kuma da Alhaji Shehu Dalhatu na TBO suka je hedikwatar APC suka mika kukansu. Uwar jam’iyyar APC ta dankawa kwamitin sasanci na Sanata Abdullahi Adamu wannan korafi domin su yi aiki a kansa.

  Ranar Litinin 29 ga watan Nuwamba 2021 wannan kwamitin ya fara aikinsa da matsalar Kano. Ya zo Kano, kuma duk wadannan shugabannin sun amince Sanata Mallam Ibrahim Shekarau shi ne zai yi magana a madadinsu. Haka kuwa aka yi. Matsayin da suka dauka guda daya shi ne basu amince da yadda aka yi shugabancin APC ba a Kano a dukkan matakai. Bukatarsu kuma a rusa abin da aka yi, a sake sabon lale a baiwa kowane mai bukata damarsa.

  Shugaban Jam’iyyar APC na jihar Kano bangaren Malam Shekarau

  Bayan sun gama zaman a Tahir Hotel ‘yan kwamitin sun bukaci bangaren Sanata Shekarau su zama cikin shiri domin za a yi zama gemu da gemu da gwamna Dokta Abdullah Umar Ganduje. Sun ce za su fara zauna wa da shi da mukarabbansa, sannan a hadu gaba daya. An samu haduwa a gidan gwamnatin Kano da tsakiyar dare na ranar Litinin har zuwa wayewar gari da asuba ranar Talata.

  Bangaren Sanata Mallam Shekarau, ya je zaman. A tawagarsa akwai Farfesa Hafizu Abubakar da Hon. Aliko Shuaibu Muktar da Dokta Umar Mustapha Musa da Injiniya Sarki Labaran da Barista Habibu Kankarofi. A wajen zaman gwamnan Kano, Dokta Ganduje yaje da mataimakinsa (Dr) Nasir Yusuf Gawuna da Sanata Kabiru Ibrahim Gaya da shugaban masu rinjaye a majalisar kasa Hon. Alasan Ado Doguwa da kakakin majalisar dokoki na Kano Rt Hon. Chidari da Alhaji Nasir Aliko Koki.

  Shugaban Jam’iyyar APC ɓangaren Gwamna Ganduje

  Sanata Abdullah Adamu ya yi bayani da farko na gabatar wa da rokon cewa alheri aka zo a kulla da kuma fatan a samu dacewa. Barista Ali Saadu Birnin Kudu ya tsefe abubuwa guda uku cewa akansu gaba daya za a gina wannan zama. Na farko an kasa samun haduwa da gwamna da Sanata Mallam Shekarau don a tattauna wanda ya kawo rashin fahimta. Na biyu kin saka masu ruwa da tsaki cikin al’amuran da suka shafi jam’iyya. Na uku an gudanar da shugabancin APC na kowane mataki babu jama’ar da suka taka rawa kuma suna da gudunmawa da za su bayar.

  Bayan wannan jawabin sai aka baiwa gwamna Ganduje dama ya yi bayaninsa. Da farko ya baiwa Mallam Shekarau hakuri, ya ce gidan gwamnatin Kano nasa ne baya bukatar iso tunda ga Kabiru Ibrahim Gaya ma ko yaushe yana shigowa. Mallam Shekarau ya ce shi ba tsarinsa bane, sai ya yi tuntuba ko an kira shi an bashi dama zai zo abu.

  Tashin farko gwamna Ganduje sai ya furta cewa ya yi alkawarin duk dan majalisar jiha dana tarayya da ‘yan majalisar dattijai kowa zai koma kan kujerarsa. Sannan na biyu kuma ya ce duk shugabannin jam’iyyar APC zabensu aka yi bisa doka kowa yana kan kujerarsa ba zai yi rawa ba. Amma za a yi sabbin nade-nade domin a shigo da wasu cikin gwamnati domin a bada kofar gyara kukan da aka yi.

  Anan ne Mallam Shekarau ya ce shi ba abin da ya kawo su ba ke nan, ba ya maganar wata kujera, yana magana akan jam’iyya da kowa yake da hakki a cikinta. Abin da suke da bukata shi ne a rushe duk wani abu da aka yi a sake sabon lale a shigo da kowa.

  Hon. Alhasan Ado Doguwa yana cikin tawagar gwamna Ganduje, ya zo da wani fayil cike da sunayen mutane wadanda a cewarsa Ganduje ya basu mukamai a gwamnati su 526 daga bangaren Shekarau. Ya yi maganganu kausasa, na rashin ladabi ga Mallam Shekarau, yana cewa shi ana yin komai da shi haka sauran yan majalisar tarayya da dattijai. Wannan ya hassala ‘yan kwamiti kuma ya kawo hayaniya da ta hargitsa zaman. A haka kuma Sanata Kabiru Ibrahim Gaya ya goya masa baya.

  Mallam Shekarau ya bada amsa cewa shi ba ya maganar mukaman gwamnati, a gurinsa nadi da saukewa na gwamna ne ba ya ja, amma jam’iyyar APC ta ‘yan APC ce kuma suna da ruwa da tsaki da hakki. Ba a zo karshen magana ba, da kansa gwamna Ganduje ya ce a ajiye wannan maganar tattaunawa akan jam’iyya tunda komai yana gaban alkali. A jira hukuncin kotu, a daidai wannan lokacin kuma an fara kiran assalatu, Mallam Shekarau da tawagarsa suka fita salla, ba su dawo ba kowa ya tafi gidansa.

  Bello Muhammad Sharada ya rubuto daga Kano

  Turawa Abokai

  RUBUTA AMSA

  Rubuta ra'ayinka
  Rubuta Sunanka a nan