Hidaya Salisu Ahmad: Gwarzuwar Ƴar Jarida Ta Shekarar 2021

587

A daidai lokacin da kwanaki kaɗan su ka rage mu yi bankwana da shekarar 2021 tare kuma da shiga sabuwar shekarar 2022, hukumar gudanarwar kamfanin Green Flame Creative masu mallakin jaridar Labarai24 da ke gudanar da ayyukanta a shafukan Intanet ta zaɓi Hidaya Salisu Ahmad, a matsayin Gwarzuwar Ƴar Jarida Ta Shekarar 2021.

Ga duk mutumin da ya ke ma’abocin bibiyar kafafen yaɗa labarai ne musamman kafar sadarwa ta rediyo to babu shakka sunan Hidaya Salisu Ahmad ba baƙo bane a gare shi, domin ta yi aiki a gidajen rediyo daban – daban a jihar Kano da ke arewacin Najeriya, ta kuma yi fice a shafukan Intanet wajen abubuwan da su ka shafi harkokin jin ƙai da tallafawa masu larurar yoyon fitsari, domin ita shugabar gidauniyar ta VVF Foundation da ke tallafawa matan da su ka haɗu da larurar yoyon fitsari.

Wacece Hidaya Salisu Ahmad?

Hidaya Salisu Ahmad ƙwararriyar ƴar jarida ce kuma gogaggiya da ta san makamar aiki. An haifi Hidaya ne a birnin Kano da ke arewacin Najeriya a shekarar 1994 a unguwar Nassarawa GRA da ke yankin ƙaramar hukumar Nassarawa.

Hidaya ta fara karatun Firamare a makarantar Firamare ta Kano Capital, bayan ta kammala kuma ta samu cigaba zuwa Sakandire ta Kano Capital wato Kano Capital Secondary School, inda ta kammala a shekarar 2011.

Bayan kammala karantun Sakandire, Hidaya Salisu Ahmed ta samu nasarar shiga mashahuriyar jami’ar nan ta Bayero da ke birnin Kano, inda ta samu digirin farko akan harkokin sadarwa da aikin jarida wato Masa Communication.

Hidaya Salisu Ahmad a bakin aiki

Bayan kammala karatun digirin farko a shekarar 2015, Hidaya ta fara aikin wucin gadi a gidan rediyon tarayya na Pyramid da ke Kano, inda daga nan ne ta fara sanin makamar aikin jarida. Ba ta ɗauki lokaci tana wannan aikin ba ta koma gidan rediyon Freedom da ke birnin Dutse a jihar Jigawa a matsayin mai hidimar ƙasa (NYSC).

Wannan Gwarzuwar ƴar jarida ta shafe shekara guda a gidan rediyon Freedom Dutse tana aikin hidimar ƙasa. Bayan kammalawa ne kuma ta sake dawowa Birnin Dabo, inda ta fara aikin wucin gadi a gidan Rediyon Dala FM inda ta shafe shekaru biyu cif a wannan tashar rediyo.

Hidaya Salisu Ahmed ta sake komawa jami’ar Bayero inda ta samu digiri na biyu a dai ɓangaren harkar sadarwar. Inda kuma tana kammala wannan karatun ne ta koma gidan rediyon Aminci FM da ke dai birnin Kano, inda aka bata shugabar sashen Labarai da al’amuran yau da kullum.

Matashiyar Ƴar Jarida, Hidaya Salisu Ahmad

Tabbas baiwa Hidaya wannan muƙami bai zo da mamaki ba musamman idan aka yi la’akari da irin gogewar da ta samu da kuma sanin aikin da ta yi. A ɗaya hannun kuma ta zamewa mata ƴan jarida musamman masu tasowa wata fitila, domin a ƙanan shekaru da ta ke da su amma ta samu nasarar kaiwa ga riƙe wannan babban muƙami.

Wata Karramawa da aka yi wa ƴar jarida Hidaya Salisu Ahmad

Babu shakka Hidaya Salisu Ahmed ƴar jarida ce da ta karɓi zamani da kuma amfani da sauyin da zamanin ya zo da shi a harkokin yaɗa labarai.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan