Mulkin farar hula bai amfanawa Najeriya komai ba – Aminu Dantata

7065

Sharerren ɗan kasuwar nan da ke jihar Kano Alhaji Aminu Alhassan Dantata ya bayyana cewa mulkin farar hula a Najeriya ya gaza domin kasar koma baya ta samu a dukkanin ɓangare na cigaba.

Aminu Dantata ya bayyana hakan ne a yau Laraba lokacin da kungiyar dattawan arewacin Najeriya karkashin jagorancin Farfesa Ango Abdullahi su kai masa ziyarar ta’aziyyar rashin Alhaji Bashir Othman Tofa a gidansa da ke birnin Kano.


Attajirin ya ce Najeriya ta ga wuce abubuwa marasa daɗi kala- kala wanda rashin kyakyawar gwamnati ne ya haifar da haka.

Haka kuma attajirin ya ce mafita kawai shi ne Najeriya tsarin mulkin ƙasar Ingila wanda hakan ne zai samar da gwamnati mai nagarta.

Tsarin mulkin da ake yi a Najeriya samfurin ƙasar Amurka wato tsarin shugaban ƙasa yana da tsauri kuma ga shegiyar tsada wajen tafiyar da harkokin gwamnati”. Attajirin ya ce tsadar tafiyar da gwamnatin a tsarin mulki mai shugaban ƙasa shi ne abin da ya haifarwa da Najeriya kalubalen da ta ke fuskanta.

Dantata ya ce akwai bukatar a sake tunani cikin gaggawa wajen ganin Najeriya ta amsa sunanta a dukkanin abubuwan da su ke da alaƙa da rayuwar al’umma, domin a halin da ake ciki ƙasar ta rasa alkibla wanda hakan ya faru ne saboda rashin manufa da kyakyawan shugabanci.

Hakazalika attajirin ya yi kira ga hukumomi da su manta da bambancin addini da na ƙabila su haɗu guri guda domin ceto Najeriya daga halin da ta tsinci kanta.

Najeriya dai na cikin shekararta ta 22 na ɗorarren mulkin dimokraɗiyya ba tare da sauyi ba, wanda shi ne mafi tsayi da aka taɓa gani tun bayan samun ƴancin kan ƙasar.

Turawa Abokai

3 Sako

  1. Gaskiya ne dubada halinda talaka ke ciki damasu hali kowa rayuwarsa nacikin dar dar,makarantu,lafiya,cigaba naxahiri kuma shugabanni basa ta AI,umma seta kansu da abinda xasu samu.kamfanoni da guraren cigaban al’umma mallakin government wasu basa aiki wasu kuma anata sayarwa, ga rashin tsaro.Allah dai ya ganar dasu sukoma tirba ta gaskiya.

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan