Sheikh Dakta Ahmad Bamba: Ba rabo da gwani ba

1863

Na sami gurbin karanta kimiyya a Jami’ar Bayero a shekarar 1992/93. Wanda ba ƙaramar sa’a na yi shiga ta a wancan lokaci ba.

Dalili kuwa na sami damar jifan tsintsaye biyu da dutse ɗaya. Saboda a lokacin kusan shekara ɗaya kacal ne da fara karatun littafin Sahihul Bukhari wanda marigayi Dakta Ahmad Bamba yake gabatarwa.

Tabbas ni da wasu abokaina da har yanzu ina tunawa da su mun sami wannan nasara tare. Ba na jin tun lokacin da na fara zama wajen karatun Bukhari a 1993 har zuwa 1998 (wato shekarar da zan tafi aikin bautar ƙasa), na yi fashin makarantar Darul Hadith ko da kwana guda.

Shekarar 1998 ta zo min da babban ƙalubale da kuma farin ciki duk a lokacin guda. Farin cikin dai na sami nasarar kammala jami’a da kuma karɓar takardar shaidar tafiya aikin bautar ƙasa zuwa Jihar Abia.

Ƙalubalen kuwa shi ne zan daina samun damar halartar karatun Hadisi, domin a lokacin babu wani abu da ake kira ‘WhatsApp’ ballantana a riƙa tura min a waya. Wayar hannun ma babu ita a lokacin.

A shekarar ne dai na sami damar halartar kwas ɗin da malaman Saudiyya suke gabatarwa a Kano, wato Daurah. Kwas ɗin da mafi yawa ɗaliban ɓangaren ƴan Islamiyya da fannin harshen Larabci ne kaɗai suke halarta. Wasu ma malamai ne ko limamai a yankunansu.

Alhamdulillah! Babban abin da ya ba ni damar shiga cikin ƴan Arabiyya a matsayina na ɗan Boko bai wuce tasirantuwa da jiɓintar karatuttukan mallam a wancan lokaci ba. (Duk da dai na yi wani ɗan karatun harshen Larabci tsakanin 1989-91).

Na yi sa’ar samun sakamako mai kyau, bayan kammala darussan. Samun wannan sakamako mai kyau shi ya sa hatta Dr. Abdullahi Saleh Pakistan, a lokacin da na kai masa sakamakon domin ya sa masa albarka ya ce, ‘ Da wannan sakamako ya kamata a tura ka jami’ar Saudiyya da take da reshe a Jamhuriyar Niger domin zurfafa karatun addini’.

Tayin da har yanzu nake nadamar rashin karɓar sa. Domin a lokacin na ce ‘Mallam ni dai na fi sha’awar kasuwanci’.

Duk wanda ya san karantarwar Dakta Ahmad BUK musamman a lokacin karatun Sahihul Bukhari ya san malam ya fi mayar da hankali wajen dasa tsaftattacciyar aƙida, fayyace su waye Sufayen gaskiya da na ƙarya da yaƙi da aƙidun Shi’a.

Dakta Ahmad BUK

Wannan ya zaburar da ni wanda har ya sa a shekarar 1997 na rubuta littafina na farko akan aƙida.

Bayan na kammala rubuce littafin, na kai wa Malam littafi har gida domin ya duba min gyare-gyare kafin a wallafa.

Na sami mallam a gidansa lokacin yana a harabar tsohuwar jami’ar Bayero. Bayan ya karɓi littafin ya ɗan bincika sai ya ce min ayyuka sun yi masa yawa. Amma ka je wajen Ja’afar ka ce ni na turo ka ya duba maka.

Haka kuwa aka yi naje na sami Shaikh Ja’afar Mahmoud Adam ya karɓeni hannu biyu ganin saƙon daga wajen Dakta ne. Haka kuwa ya duba littafi na dawo bayan sati ɗaya na karɓa.

Dakta Ahmad BUK mutum ne mai sauƙin kai da kuma haba-haba da ɗalibansa, ba shi da nuna isa ko ƙadan. Malami ne mai sakin jiki da na ƙasa da shi ba tare da tsangwama ba.

Wata rana kamar yadda muka saba kai masa ziyara ( lokacin yana gidansa dake Ɗorayi Ƙarama). Mun haye kujeru muna ta hira da ɗan jefa tambayoyin ana ba mu amsa. Kwatsam sai Malam Ja’afar Mahmoud Adam ya yi sallama ya shigo.

Yana shigowa sai ya zauna a ƙasa kan kafet ya gaishe da malam suka fara tattaunawarsu. Mu kuwa sai muka yi tsuru-tsuru a bisa kujeru, ganin a ce hatta malam Ja’afar da ya zo ya zube a ƙasa, mu kuma a su wa muna bisa kujera?

Haka dai kunya ta ishe mu. Ƙarshe muka katse tattaunawarmu da malam muka yi masa sallama muka bar shi da mallam Ja’afar.

Haɗuwata da mallam ta ƙarshe bai wuce sati uku kafin rasuwarsa ba, na gaishe shi kamar yadda a ka saba ya amsa ya ce ;”Kun yi taro lafiya? Allah Ya ba su zaman lafiya.” Ashe haɗuwar ƙarshe kenan.

Bayan na sami labarin malam yana asibiti cikin mawuyacin hali a ranar Alhamis, mun dai ci gaba da addu’ar Allah Ya ba shi lafiya.

Kwatsam ranar Juma’a da misalain ƙarfe 10:25 na safe sai na ga waya aka ce Allah Ya karɓi ran malam.‘Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un.’ Abin da na iya furtawa kenan. Malam lokaci ya yi.

Duniyar Hadisi ta sami girgiza.

Abin da masana suke faɗi shi ne duk faɗin duniyar Bahaushe babu wani malami da ya karantar da tarin littafan Hadisan da ya karantar a bainar jama’a har na tsawon shekaru kusan 30 babu fashi.

Karantarwar malam a shekaru 10 na farko ya fi ƙarfafa bayani a kan riƙo da sunnah, yaƙi da aƙidun Sufaye da Shi’a. Koyar da tarbiyya da ƙarfafa mutane su koma su karanci addini tsaftatacce.

A shekarun karantarwarsa na ƙarshe kuwa, ƙoƙari ne wajen jawo hankulan al’umma su rage nuna banbance-banbance, da cene-nace a kan abubuwan da aka yi saɓani a kai, tunda ba a kan aƙida ba ne.

Lallai Allah (SWT) Ya ɗauke ran malam a daidai lokacin da al’umma ba ta gama ƙoshi ko buƙatuwa da ilmantarwarsa ba. Ba su gama ɗibar tarbiyyar da yake bayarwa gare su ba.

Al’umma ta yi rashin uba, haziƙin mutum mai hangen nesa, dattaku, kawaici da tarin ilmi. Babban tashin hankalin shi ne, shin waye zai gaji Dakta Ahmad Bamba?

Anya za a sake samun wani jajirtacce kamarsa?

Ƙwarewarsa, tarin ilminsa, da dattakunsa?

A nan Kano zai ɓulla ko a wata shiyya ta Arewacin ƙasar nan?

Ko a wata ƙasa ta daban ne?

Allah ne masani.

Bahaushe dai ya ce, ba rabo da gwani ba…

Allah Ya gafarta wa malam, Ya yafe kurakurensa Ya ba shi gidan Aljannah.

Mu kuma Allah Ya ba mu haƙurin rashin sa, Ameen thumma ameen.

Ado Abdullahi ya rubuto daga Kano-Nijeriya.

Turawa Abokai

2 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan