Gajeruwar Nasiha: Abin da zai faru a ranar Lahira

  267

  Yawancin darussa da muke gani kullum a rayuwa su ne abubuwan da zasu faru a ranar LAHIRA. Za ku ga mutane a duniya sun sami ilimi, wadata, ɗaukaka da sauran ni’imomi, su na ta ba da sha’awa sun zama abin alfahari, katsam sai ka ji sun ruguzo babu sauran daraja (misali Abba Kyari da makashin Hanifa).

  A lahira ma haka za’a sami akasarin mutane sun shige wuta bayan a duniyar nan muna ganinsu abin sha’awa, musamman malamai da wasu manyan al’umma. Allah ya yi mana bayaninsu cikin suratul Munafiqun cewa Q63:4 “Kuma idan ka gansu sai jikunansu su baka sha’awa kuma idan sun faɗa zaka saurara ga maganarsu”.

  Yawancin manyan mutane sun faɗa cikin wannan jeri domin Allah yayi musu ni’imomi da kowa ke sha’awa kuma ana jin maganarsu. Amma a zahiri holoko ne su a wajen Allah domin basa ƙoƙarin taimakawa na ƙasa da su da niimar da Allah ya ara musu kamar yadda aya ta bakwai a surar ta fada.

  Yawancinsu a nan ƙasar zaka ga suna fafutukar a basu mulki amma da zarar sun samu sai cin amanar talaka.

  Wallahi ƴan uwa mu sani cewa duk iliminka, dukiya ko mulki ba za su tsinana maka komai a wajen Allah ba sai ka aiwatar da su wajen hidimtawa al’umma (Allah bai taɓa yiwa wani mutum wata ni’ima don kansa kawai ba).

  Mutum guda ne zai tsira a gaban Allah a ranar lahira, kamar yadda yace, wato wanda ya zo masa da “Ƙalbin Saleem”. Duk mai tsarkakakkiyar zuciya Allah ba zai taɓa barinsa ya taɓe a duniya da lahira ba.

  Ita tsarkakakkiyar zuciya ba ta hassada da ƙyashi, ba ta rowa da mugunta, a kullum alhairi take hari don haka a duniya da lahira take gamo da alhairi.

  Muguwar zuciya kuwa komai aikin alherinta na zahiri zaka samu babu ikhlasin ubangiji a ciki na Hakika don haka sai dai ta sami wani gajeren yabo a wajen mutane na wani taƙadirin lokaci kafin Allah ya wofintar da wannan yabon.

  Wasu, irinsu Abba Kyari da masu mulki mayaudara, tun a duniya Allah ke watsa musu ƙasa a fuska amma wasu sai an je lahira. Don haka duk wanda ke son tsira a duniya da lahira wajibi ya tsarkake zuciyarsa, ya kasance cikin jerin masu “Ƙalbin Saleem”. Allah ya ba mu iko.

  Ali Abubakar Sadiq ya rubuto daga Kano – Najeriya.

  Turawa Abokai

  RUBUTA AMSA

  Rubuta ra'ayinka
  Rubuta Sunanka a nan