Fitila: APC ta kama hanyar wargajewa, Tauraruwar Madugun Kwankwasiyya na daf da shiga kusufi

  1853

  A wannan makon zamu fara sharhin namu ne da dambarwar da ke faruwa a jam’iyyar APC, ga dukkanin masu bibiyar al’amuran siyasa na sane da yadda rikice-rikice ke damun jami’yyar kama daga rikicin shugabanci a matakin tarayya har zuwa rikicin jihohi wadda ya – ƙi – ci – ya ƙi cinyewa har kawo yanzu da APC ɗin ke dab da gabatar da babban taronta na ƙasa domin zaɓen shugabannin da za su jagoranci ragamar ta zuwa kakar zaɓe mai zuwa. Idan mai karatu zai iya tunawa, a baya rikicin da ya dabibye Jami’yyar ne yayi sanadiyar korar shugaban ta na farko wato Mista John Odigie Oyegun bayan tsunduma APC ɗin da yayi a cikin rikice-rikice musamman na cikin gida wanda ya haifarwa da jami’yyar rasa wasu jihohi masu tarin yawa. Wannan ne ya sa ganin yadda APC din ta ke neman wargatsewa ya sa shugaban ƙasa ya ba da umarnin tsige shugaban inda a shekarar 2018 aka maye gurbinsa da tsohon Gwamnan jihar Edo, wato Comrade Adams Oshiomhole.

  Zuwan Comrade Oshiomhole a matsayin shugaban APC ya bawa al’umma da dama musamman mabiya jami’yyar ƙarfin gwiwar ganin za ta iya dawowa kam tafarki madaidaici. Sai dai kash, ba a daɗe da zuwan na sa ba sai rikice-rikice musamman a lokacin fitar da ƴan takarkari ya sake kunno kai cikin jam’iyyar. Kaɗan daga cikin manyan asarar da tsohon shugaban APC wato Oshiomhole ya yiwa jam’iyyar sun haɗa da rasa kujerar gwamnan jihar Edo bayan yayi rigima da Gwamna mai ci, wato Godwin Obaseki, wanda daga ƙarshe ya fice daga jam’iyyar ta APC ya koma jam’iyyar PDP kuma ya ka da ɗan takarar da shi Oshiomhole ɗin ya tsayar. Sai kuma wani rikici da ya sake ɓarkewa a cikin jam’iyyar reshen jihar Imo tsakanin Gwamna mai ci a waccan loakcin wato Rochas Okorocha da Gwamna mai ci a yanzu wato Hope Uzodinme, wutar da har yanzu tana ci gaba da ruruwa tsakanin ƴan siyasar guda biyu. Sai dai duk waɗannan ba su sa jagororin jam’iyyar sun hankalta ba kuma sun ɗau matakin da ya da ce akan tsohon shugaban jam’iyyar har sa da ya yiwa APC ɗin asarar dukkanin kujerun da ta ci a kakar zaɓen shekarar 2019, misali a jihar Zamfara bayan da ya haɗa rikicin siyasa tsakanin Gwamna Abdul’aziz Yari da Sanata Kabiru Garba Marafa sannan mahukunta a jam’iyyar suka ɗauki mataki sallamarsa daga shugabancin gaba ɗaya.

  Magoya bayan jam’iyyar APC a lokacin wani taro

  Jim kaɗan da korar Adams Oshiomhole daga shugabancin ne sai APC ɗin ta kafa shugabancin riƙon ƙwarya ƙarƙashin jagorancin Gwamnan jihar Yobe, wato Mai Mala Buni. Tun farkon shugabancin nasa, al’umma da dama sun ta ƙorafi kan yadda aka bashi jagorancin jam’iyyar ganin cewa shi gwamna ne mai ci. Amma dai wannan bai hana shi riƙon APC ɗin ba har na tsawon kusan shekaru biyu Kafin daga bisani wasu jiga – jigai a cikin jam’iyyar su jagoranci tsige shi daga shugabancin kamar yadda Gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasiru El-Rufa’I ya shaidawa kafar talabijin ta Channels. Wannan kora da aka yiwa Buni ta sake tayar da wata ƙura tare da raba kawunan ƴan jam’iyyar inda mutane da dama musamman ƴan APC ke tofa albarkacin bakinsu. Ko a ranar asabar ɗin da ta gabata sai da aka jiyo shugaba Muhammadu Buhari na kira ga ƴan jam’iyyar da su gu ji cin zarafin juna, da yin abinda ka iya jefa APC ɗin cikin ruɗani ko kuma abinda ya samu jam’iyyar PDP a shekarar 2015. Nan zamu ajiye wannan batu, zamu ci gaba da bibiyar lamarin dan ganin yadda zata karke game da shugabancin APC maja.

  Bari mu dawo jihar Kano mu yi duba da halin da siyasar Madugun Ɗariƙar Kwankwaasiya ta ke ciki. A haƙiƙanin gaskiya siyasar madugun Kawnkwasiya ta fara shiga halin ni ƴa su, domin kuwa madugun tuni ya raba gari da babbar jam’iyya mai hamayya, PDP bayan da ya ke zargin ba a yi masa adalci a shugabancin jam’iyyar ba. Wannan ce ta sa a kwanankin baya ya kafa wata ƙungiya da ya ke tunanin zai yi amfani da ita domin cimma burinsa na zama shugaban Najeriya a babban zaɓen shekarar 2023 da ke tafe.

  Jim kaɗan bayan kafa wannan ƙungiya sai kuma aka jiyo madugun ya haɗa kayansa ya koma jam’iyyar New Nigerian People’s Party (NNPP) tare da wasu mabiyansa. Sai dai abinda ya bawa al’umma mamaki shi ne yadda wasu daga cikin jiga – jigan tafiyar Kwankwasiyyar kamarsu Dakta Yunusa Adamu Dangwani da Abubakar Nuhu Danburan da Yusuf Bello Ɗambatta, da Barista Hadiza Adedo da kuma Aminu Dala sun ƙi yin mubaya’a ga Madugun na su. Wannan dai masana na ganin cewa ba ya rasa nasaba da ƙaƙaben da waɗannan mabiya suke zargin madugun na su ya na yi musu musamman a lokacin tsayar da ƴan takarkaru.

  Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso

  To ko shin mai wannan kaura ta Sanata Rabi’u Kwankwaso ke nunawa a game da tafiyarsa ta sa? Tabbas zamu iya cewa siyasar madugun ta fara dusashewa, kuma tabbas in dai a wannan karo bai yi wani abin a zo a gani ba musamman na kafa gwamnati a jihar Kano inda ake ganin nan ne kawai yake da magoya baya masu yawa, to shakka babu za’a rufe shafinsa a siyasar Najeriya daga kakar zaɓen 2023.

  Bari mu ƙarƙare wannan sharhi namu da harkokin tsaro da hare-haren ƴan bindiga wadda ya ƙi ci ya ƙi cinyewa a yanki Arewa masu Yamma. A makon da mu ka yi bankwana da shi ne aka sami labarin cewa ƴan bindiga sun kai hari kan motacin mataimakin Gwamnan jihar Kebbi inda suka halaka wasu jami’an tsaro da ke kare lafiyar mataimakin Gwamnan. Hakazalika a jihar ta Kebbi dai an samu labarin yadda ƴan bindigar su ka kashe masu tsaro na sa kai fiye da guda 60 tare da wasu sojoji wanda hakan ya haifar da zanga-zanga daga matan sojojin da aka kashe.

  Wannan batu na tsaro tabbas babban al’amari ne wanda ya kamata a ce mahukunta sun tashi tsaye haikan tare da mayar da hankali domin kawo ƙarshen wannan ta’asa da ƴan bindigar ke aikatawa. Domin kuwa idan har ƴan bindigar za su iya kaiwa motocin mataimakin gwamna hari har su kashe wasu daga cikin masu ba shi tsaro to lallai al’umma suna cikin tashin hankali.

  Ali Sabo ɗan jarida ne kuma mai yin sharhi akan al’amuran yau da kullum, ya rubuto daga Kano – Najeriya.

  Turawa Abokai

  RUBUTA AMSA

  Rubuta ra'ayinka
  Rubuta Sunanka a nan