Rashin Tsayar Da Gemu A Afghanistan Ka Iya Sa Mutum Ya Rasa Kansa

482

Hukumomi a Afghanistan sun fara tilasta wa ma’aikatan gwamnati tsayar da gemu da kuma sanya sutura irin ta addinin Musulunci.

Jami’an gwamnatin Taliban sun tsaya a gaban ofisoshin gwamnati da nufin duba ko tsawon gemun ma’aikatan ya kai yadda hukuma ta bada umarni.

Haka kuma, gwamnatin ta kafa dokar cewa dole kowane ma’aikaci ya yi shiga irin ta addinin Musulunci.

Ma’aikatar Yaɗa Kyawawan Halaye da Hana Aikata Laifuka ta Afghanistan ta gargaɗi ma’aikatan gwamnati cewa za su iya rasa ayyukansu idan ba su mayar da hankali kan waɗannan dokokin ba, kamar yadda BBC Hausa ta rawaito.

Waɗannan dokoki na tsayar da gemu da sanya suturar Musulunci suna cikin sabbin dokokin da gwamnatin Taliban ta kafa a kwanan nan.

A makon da ya gabata ne gwamnatin ta rufe makarantun mata na sakandire.

Haka kuma, gwamnatin Taliban ta hana mata yin tafiye-tafiye a jiragen sama na cikin gida ko masu zuwa ƙasashen waje ba tare da muharrami ba, ta kuma hana cuɗanyar mata da maza a wuraren shaƙatawa.

AA Agusta, 2021 ne Afghanistan ta ƙwace mulki bayan da sojojin Amurka suka bar ƙasar bayan sun shafe shekara 20 suna yaƙi.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan