Sabbin Malaman makarantar sakandare da gwamnatin jihar Kaduna ta dauka tun a watan yulin shekarar 2021, sun koka kan yadda gwamnatin ta kyalesu, ba wajen aikin ballantana samun albashi.
Wata daga cikin sabbin malaman, a zantawarta da Daily trust ta bayyana takaicinta kan yadda ta Ajiye aikinta don samun wannan sabon aikin, amma yau wata 9 kenan ba wurin aiki ba albashi.
Muna Miko Kokan Bara A Taimaka A Bamu Shugabancin Nijeriya A 2023 —Kabilar Igbo
“Na karbi takardar fara aiki na a ranar 19 ga Yuli, 2021, amma har yanzu, da ni da sauran sabbin Malaman sama da 7,000 ba musan wurin aikin mu ba.” Inji ta.
A watan Janairun 2019 mutane 62,000 ne suka zana jarabawar neman karantarwa, inda daga baya aka zakulo 14,000 a matsayin wadanda za a tantance don yin aiki a karkashin Hukumar Kula da Malamai ta Jihar Kaduna (KSTSB). Daga cikin wannan adadin ne aka dauki mutane 7,600 aiki.
Watanni 9 bayan an ba su takardar shaida a matsayin ma’aikatan gwamnati, sabbin malaman da aka dauka sun ce har yanzu ba a tura su wata makaranta don fara aiki ba, duk da cewa suna da burin bayar da gudunmawarsu wajen ci gaba da kuma sake fasalin tsarin ilimi a jihar.
Yayin da Daily trust ta ziyarci Hukumar Kula da Malamai ta Jihar Kaduna a ranar Asabar don jin ta bakinta game da lamarin, an shaida wa wakilin cewa Shugaban Hukumar, Adamu Makadi yana wani taro, inda daga nan aka tura shi ga Ma’aikatar Ilimi.
Da isarsa ma’aikatar, bayan tuntuba, sai akace masa kwamishiniyar ilimi, Halima Lawal, tana cikin wani taro.
Ba ta amsa kiran waya ba da sakonnin da aka aike mata kan batun a lokacin haɗa wannan rahoton.