Tsohon gwamnan jihar Kano Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya ziyarci tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo a gidansa da ke Lagos.
Shafin Facebook na Sanata Rabi’u Kwankwaso ne ya wallafa hotunan ziyarar a shafin sa na Facebook.

Ziyarar dai ta zo kwana ɗaya da Sanata Kwankwason ya biya naira miliyan 30 domin sayen fom na yin takarar mukamin shugaban ƙasa a ofishin jam’iyyar NNPP da ke birnin tarayya Abuja.
Sanata Kwankwaso ya taɓa rike mukamin ministan tsaro a zamanin gwamnatin Obasanjo.
.
Turawa Abokai