A yau ne ma’aikatan Najeriya su ka bi sahun sauran ma’aikata a ƙasashen Duniya, domin bikin Ranar Ma’aikata. Bikin na yau dai ya na zuwa ne a lokacin da ma’aikata a jihar Kano ke kokawa akan matsalolin da su ke fuskanta game da albashi.
Tun da farko an kebe ranar 1 ga watan Mayu ne duk shekara matsayin ranar ma’aikata a fadin duniya.
Bikin ya kan baiwa ma’aikatan damar fitowa su bayyana bukatunsu da damuwarsu ga gwamnatocinsu ta hanyar gudanar da gangami tare da laccoci da akasari kungiyoyin ma’akatan daban-daban kan fito su gabatar.
Sai dai ma’aikata a Kano sun bayyana cewa su na fuskantar matsaloli da dama da suka haɗa da yanke albashi, da rashin kulawa wajen aiki, da rashin ƙarin girma da rashin bayar da horo ko karawa juna sani da kuma rashin biyan albashin akan lokaci.
Haka kuma wasu ma’aikata sun bayyanawa Labarai24 ra’ayoyinsu game da wannan rana, da cewar ko shakka babu su na farin ciki da wannan rana domin ko ba komai an girmama ma’aikata ta hanyar ba su rana guda da ta zama ta su.
“Gaskiya muna farin ciki da bikin ranar ma’aikata ta duniya, sai dai mu a nan jihar Kano gwamnati sam ba ta ɗauke mu da muhimmanci ba. Domin irin wani wulakancin da bama fuskanta daga wannan gwamnati”.
“Kama daga kan yanke albashi da rashin biyan albashin akan lokaci da kuma uwa uba rashin tabbas idan aka kammala aikin” – In ji wani ma’aikaci da ya bukaci a sakaye sunansa.
Ita kuwa wata ma’aikaciya a hukumar tattara kuɗin shiga ta jihar Kano da buƙaci a sakaye sunanta kokawa ta yi akan yadda ake shafe fiye da kwanaki 35 kafin a biya albashi a wannan ma’aikatar.
“A hukumar tattara kuɗin shiga ta jihar Kano, muna ɗaukar kwanaki 35 zuwa 37 kafin a ce an biyamu albashi, wanda hakan babbar illah ce ga duk wani ma’aikaci musamman mai iyali”.
“Ya kamata gwamnatin jihar Kano ta samar da kyakkyawan tsari ga ma’aikata da za su san cewa tabbas su na hidimtawa al’umma”.
Ma’aikata dai a Kano sun jima suna kokawa da irin halin kuncin da su ke shiga na rashin kulawa da kyautata jin dadin su daga hukumomi bayan kammala aiki.