Rashin Biyan Albashi: Ma’aikatan gidan rediyon Liberty a Kano na cigaba da ajiye aiki

589

Wani rahoto da jaridar Nigerian Tracker da ake wallafawa a intanet ya bayyana cewa kimanin shugabanni bakwai da ke jagorantar ɓangarori daban-daban a gidan rediyon Liberty a jihar Kano, su ka ajiye aikin su kamar ɗaya daga cikin wanda abin ya shafa ya tabbatarwa da jaridar faruwar lamarin.

Da suke bayyana dalilansu na ajiye muƙaman na su ma’aikata da shugabannin da suka haɗa da shugaban sashen kula da na’urori, Shugaban sashen Labarai da kuma Shugaban kula da ɗakunan yaɗa shirye-shirye, sun ce ajiye aikin na su na zuwa ne biyo bayan rashin kyakykyawan tsari da suke fuskanta a gidan rediyon da rashin kyawun yanayin gudanar da aiki da kuma sauran abubuwanda suka shafi kafar a nan Kano.

Kazali ya kuma ƙara da cewa kimanin watanni uku ke nan ma’aikatan gidan rediyon su ka shafe suna jiran albashi daga mahukuntan gidan rediyon.

Sai dai shugaban gudanarwar gidan rediyon na Liberty reshe Kano, Aminu Nuruddeen Amin, ya bayyana cewa ma’aikatan ba su ajiye aikin na su ba kan wancan dalilin da ake zargi sai dai kafar ta ɓullo wani yanayi ne da zai inganta alaƙarsu da masu sauraro.

Aminu ya kuma ce hukumar gidan ta umarci ma’aikatan na ta ne kawai da su ɗauki wani hutu zuwa wani lokaci da za a daidaita lamarin.

Ya ƙara da cewa sun bawa wasu daga cikin ma’aikatan dama da su nemi wani aikin na daban kuma a lokaci ɗaya suna aiki da Liberty ɗin.

Liberty ce kaɗai ta ke fuskantar wannan matsalar?

Akwai gidan rediyo a birnin Kano fiye da guda ashirin (20) kuma a cikin wannan adadi idan ka cire gidan rediyon Bello Dandago da ke kan zangon AM da kuma FM da gidan rediyon ARTV da na Pyramid FM Madobi da su ke mallakin gwamnatin jihar Kano da kuma gwamnatin tarayya, duk sauran na ƴan kasuwa ne da su ka kafa domin su mayar da Taro zuwa Sisi.

Haka kuma mafi yawa daga cikinsu suna samun tsaiko wajen biyan ma’aikata albashi wanda ake alaƙanta hakan da rashin samun kuɗin shiga, wasu kuwa suna samun isassun kuɗaɗen kuɗin shiga sai dai ana zarginsu da take haƙƙin ƙananan ma’aikata daga manya.

A shekarar 2021 sai da ma’aikatan gidan rediyon Vision da ke birnin Kano su ka ajiye ayyukan su sakamakon rashin kyakkyawan yanayin gudanar da aiki da kuma rashin biyansu albashi da sauran haƙƙoƙinsu.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan