A daidai lokacin da ƴan siyasa a jam’iyyar APC musamman waɗanda su ka fito daga yankin kudancin Najeriya ke cigaba da bayyana aniyarsu ta tsayawa takarar kujerar shugaban ƙasar a zaɓen 2023.
Sai ga shi Gwamnan jihar Jigawa, Muhammad Badaru Abubakar ya garzaya sakatariyar jam’iyyar a jiya Laraba, inda ya yanki fom ɗin neman APC ɗin ta sahale masa takarar shugabancin Najeriya a kakar zaɓe mai zuwa.
Gwamna Badaru wanda ya fito shiyya ɗaya da shugaba Muhammadu Buhari, ya sayi fom ɗin ne a dai-dai lokacin da manyan jam’iyyun Najeriya guda biyu PDP da APC su ke muhawara akan wacce shiyya ya kamata su kai takarar shugabancin ƙasar a 2023.
Haka kuma Gwamnan ya yi wata ganawa ta musamman da Shugaban jam’iyyar na ƙasa Sanata Abdullahi Adamu a gidansa da ke Abuja jim kaɗan bayan bayyana kudirin na sa.

Sai dai wata majiya daga fadar gwamnatin Jigawa da ta buƙaci a sakaye sunanta ta shaidawa Labarai24 cewa umarni ne daga fadar shugaban ƙasa a ka baiwa gwamnan dan neman shugabancin a jam’iyyar ta APC.
“Duk abin da ka ga mun yi akwai lissafi, domin shi mai girma Gwamna ba zai taɓa yin abu babu lissafi”.
Kudurin na Gwamna Badaru na zuwa a lokacin da ake raɗe – raɗin akan jam’iyyar ta APC za ta sake dawo da takara shiyyar Arewacin Najeriya.
Haka kuma ana ganin Gwamna Muhammad Badaru Abubakar na da tasiri sosai a gurin shugaba Muhammadu Buhari da wasu masu faɗa a ji a cikin jam’iyyar APC.