A ƙarshe Malam Ibrahim Shekarau ya sansanta da Gwamna Ganduje

438

Wani rahoto da jaridar Daily Nigerian ta rawaito ya bayyana cewa tsohon Gwamnan Kano, Malam Ibrahim Shekarau ya sansanta da Gwamna mai ci Dakta Abdullahi Umar Ganduje.

Idan za a iya tuna wa, jam’iyyar APC ta dare gida biyu a Kano tun bayan zaɓen shugabannin jam’iyyar a matakin jiha, inda Sanata Shekarau ya jagoranci ɓangare ɗaya, ya kuma tsayar da Alhaji Ahmadu Haruna Zago a matsayin shugaban jami’yya, shi kuma Abdullahi Abbas, a matsayin shugaban jam’iyyar na ɓangaren Ganduje.

Haka a ka ci gaba da tafiya har ta kai ga ɓangarorin sun dangana ga kotun ƙoli, inda yanzu a ke jira ta yanke hukunci.

Sai dai kuma a bisa rahoton da jaridar ta wallafa, tuni dai Shekarau ya zagaye ya sasanta da Ganduje, kuma har yanki fom ɗin sake tsaya wa takarar Sanata, bayan tabbatar masa da dawo masa da takarar sa

Haka kuma Malam Shekarau da Ganduje sun raba dare a ranar Litinin, har zuwa awannin farko na Talata su na wata ganawar sirri domin sulhunta wa, inda daga ƙarshe dai a ka yarda cewa Shekarau zai koma kujerarsa ta Sanata.

Haka zalika an jiyo cewa sansanta war ta biyo bayan kiran da Shugaban APC na Ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu ya yi na cewa a sansata da duk wani tsohon Gwamna da ke Majalisar Dattawa a kuma sake bashi takara a 2023.

A yau Juma’a ne kuma Shekarau da Ganduje za su rankaya zuwa Abuja domin gana wa da Shugaban na APC na Ƙasa domin sake ƙarfafa sulhun da a ka yi tsakanin shugabannin biyu.

Tuni dai wannan lamari ya harzuƙa magoya bayan G-7, har ya haifar da cecekuce, musamman tsakanin ɓangaren Sanatan Kano ta Arewa, Barau Jibrin da kuma na Malam Ibrahim Shekarau ɗin.

Sai dai kuma Kakakin Shekarau, Sule Ya’u Sule, ya musanta batun cewa tsohon gwamnan ya bar ɓangaren G-7.

Ya shaida wa jaridar Daily Trust cewa har yanzu Shekarau shi ne shugaban G-7, inda ya ƙara da cewa har yanzu ɓangaren na tafiya tare kuma duk wani mataki a na ɗauka ne tare.

Sule ya ƙara da cewa fom ɗin da Shekarau ya siya ba wai yana nufin ya bar ɓangaren bane, inda ya ce sauran masu ra’ayin takara ma a G-7 duk sun sayi fom domin lokacin da a ka sanya da farko za a rufe sayar da fom ɗin yau ne Juma’a, kafin daga bisani jam’iyar ta ƙara kwanakin rufe sayar da fom ɗin.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan