Annoba: Kwalara tayi sanadiyyar rasa ran kimanin mutum 54 a Nijeriya-NCDC

333

Hukumar daƙile cututtuka masu yaɗuwa ta ƙasa NCDC ta bayyana cewa kimanin mutum 54 a sassan jihohin ƙasar nan 19 ne su ka mutu sanadiyyar annobar Kwalara, haɗi da samum sama da mutane 1,862 da suke dauke da cutar a wannan ƙasa.

Rahoton wanda hukumar ta NCDC tatattara tsakanin watan janairun farko wannan shekarar zuwa farkon watan Mayun shekarar ta 2022.

NCDC ta ƙara da cewa kusan mutum 1,800 ne ake tsammanin sun kamu da cutar a ƙananan hukumomi 77 dake sassan jihohi 16 na ƙasar nan.


Jihohin da annobar Kwalara ta ɓarke sun haɗa da Abia, Adamawa, Akwa Ibom, Bauchi, Bayelsa, Borno, Cross River, Katsina, Kebbi, Kwara, Lagos, Nasarawa, Ondo, Rivers, Taraba, da kuma Zamfara.

Haka kuma alƙaluma sun nuna cewa mafi yawancin masu ɗauke da wannan cutar yara ne wanda shekarun su ba su gaza 5 ba zuwa sama a duniya.


Daga cikin yaran da annobar ta kama sun haɗa da kaso 50 na mata inda ragowar kashi 50 ɗin su ka zamto maza, a yayin da jihohi uku daga cikin jihohi 16 su ka ɗauki kaso 75 na masu ɗauke da cutar.


Jihohin dai sun haɗa da Taraba, mai ɗauke da mutane 615, sai Cross River, 593 da kuma Katsina, da ke da mutane 134.

Hukumar lafiyar ta ƙara da cewa daga farkon wannan shekara zuwa watan Mayu, an samu mutane 30 a sauran jihohi 12.

Ita dai wannan cuta ana kamuwa da ita ne ta hanyar yin amfani da wuri mara tsafta ko kuma cin abu ko sha mai ɗauke da kwayar ta kwalara, inda cutar take galabaitar da masu ɗauke da ita wani lokacin har ta kai ga rasa rai.

Indai za a iya tunawa annobar Kwalara tayi sanadiyyar mutuwar mutum sama da 3,604 sama da adadin mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon annobar COVID-19 kamar yadda babban daraktan Hukumar NCDC Dakta Ifedayo Adetifa, ya bayyana.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan