Bayani kan tattalin arzikin Najeriya a hannun shugaba Buhari daga 2015 – 2021

  296

  Na Daya:

  A yau bashin da ake bin Najeriya, na jihohin kasar nan dana gwamnatin tarayya ya kai naira tiriliyan 42. Abin da shugaba Muhammad Buhari ya gada daga gurin Goodluck Jonathan shi ne Naira tiriliyan 11.

  Na Biyu:

  Babban bankin Najeriya CBN karkashin jagorancin Godwin Emeifele, ba aikin samar da hanyoyi n bunkasa arziki da kula da hawan farashi yake ba, yanzu babbar hanyar yadda yake samar da kudi shi ne ya buga naira kudin Najeriya, ya watsota gari, wato abin da masana ke kira ‘Ways and Means’ sannan in ya buga, sai ya baiwa gwamnatin tarayya bashi. Yanzu haka bashin da CBN ta baiwa FG ya kai naira tiriliyan 19. Wannan bashin ba ya cikin lissafin basussukan da FG da jihohi suka ciwo.

  Na Uku:

  A jere-jere a shekara shida duk kudaden da Najeriya take samu na haraji daga fetur wato ‘oil’ da harajin abin da ba fetur ba, wato ‘non-oil’ ana daukarsu kaco-kam, kusan Kashi 96, ana aika wa da su waje da nan cikin gida domin biyan kudin ruwa na bashin da ake ciwo wa. A shekarar 2021 Najeriya ta samu kudi tiriliyan hudu da rabi daga haraji da ake matsowa a Kamfanoni da ma’aikatu da jama’a da sauran hanyoyi, kuma ta ranto tiriliyan uku da rabi, amma ta biya kudin ruwa tiriliyan hudu ba kadan da kudin da ta tara.

  Na Hudu:

  Halin da ake ciki, duka ma’aikatan gwamnatin tarayya ba a iya biyansu albashi na wata-wata, haka hakkokin ‘yan fansho ba ya iya fitowa sai an ci bashi. Ana biyan kusan tiriliyan uku duk shekara. A 2016 an kashe tiriliyan biyu ba kadan, a 2017 an kashe tiriliyan biyu da doriya, a 2018 da 2019 an kashe tiriliyan biyu da rabi da 2020 da shekarar 2021 an kashe tiriliyan uku. A bana 2022 ana sa rai kudin zasu kai tiriliyan hudu. Kusan kashi 73 na duk kudin da ake samu ana kashe su wajen biyan ma’aikatan gwamnatin tarayya wanda suke Federal Civil Service su dubu 400.

  Na Biyar:

  Hawan mulkin PMB man da ake hakowa kullum ya kai ganga miliyan daya da dubu 800. Zuwa watan jiya Mayu 2022 abin da ake fitarwa ganga miliyan daya da rabi. Kudin da aka sayar da wannan danyen man da su ake sauran hidimomin kasa. A shekara bakwai na Buhari kuma ministan man fetur, ko sau daya matatun man fetur na Fatakwal da Kaduna da Warri basu tace mai sun kai waje ba, amma an kashe musu kudin gyara da albashi kusan naira biliyan 954. Haka kuma duk fetur din da ake hakowa a kasar nan a yankin Inyamurai kashi 95 sace shi ake. A takaice ma da manyan kamfanonin da suke hada-hadar hako fetur a Najeriya sun gudu, sun koma da kadarorinsu wasu kasashen ketare.

  WANNAN alkaluman fa, abin da suke gaya mana, kasarmu Najeriya tana cikin babbar matsala.

  Bello Muhammad Sharada ya rubuto daga Kano – Najeriya

  Turawa Abokai

  RUBUTA AMSA

  Rubuta ra'ayinka
  Rubuta Sunanka a nan