Irin hidimar da Mohammed Salah ya ke yiwa ƙauyensu

96

Mo Salah dai ya sha yin abubuwan al’ajabi ga mutanen kauyensa Nagrig. Ya gina asibiti, makaranta, wajen wasanin matasa, sannan ya samar da motocin ɗaukar marasa lafiya a kauyensa.

wajen wasannin matasa

Ya gina kamfanin samar da ruwan sha na dalar Amurka 450,000 domin samar da ruwan sha ga jama’arsa sannan duk wata yana ba da gudummawar Fam 3,500 ga iyalai marasa galihu.

marasa galihun da Salah ya ke taimakawa

Ya ba da gudummawar fam miliyan 2.5 don maganin cutar kansa a Masar yayin da sashin motar daukar marasa lafiya ke yi wa mutane 30,000 hidima.

Domin samun kayan aikin likitanci na zamani, Salah ya ba da gudummawar fam 50,000 ga asibitin jami’ar Tanta. 

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan