Lafiya: Nijeriya ce kan gaba da kaso 50 cikin 100 na masu ɗauke da cutar Sikila a Duniya

72

Hakan dai ya fitone ta bakin jama’a mai kula da sashen cututtukan jini wato ‘Department of Hematology Aminu Kano Teaching Hospital AKTH’, Dr. Aisha Amal Galadanchi Aƙilu, a ci gaba da bukukuwan ranar Amosanin Jini ‘ Sikila’, haɗi da bada Agajin Jini ‘Blood Donor” ta duniya wacce majalisar ɗinki duniya ta ware a dukkanin watan Yuni, domin nuna muhimmancin bayar da agajin dama muhimmancin gwaji jini ‘Genotype’.

Kan wannan rana ce sashen kula da cututtukan jini na Asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano, su ka shirya gangamin wayar wa da mutane kai kan muhimmancin gwajin jini kafin aure da ƙaddamar da bayar da gudun mawar jini daga al’umma.

Yadda wani bawan Allah ke bada gudunmawar jini

Lalular Amosanin Jini, wacce aka akafi sani Sikila wato ‘Sickle cell’ a turance, cutace da masana lafiya ke ci gaba da wayarya da al’umma kai dan gane da illolin da take haifar wa musamman a zaman takewar auratayya.

Dr. Aisha Amal, cewa tayi ”kimanin kaso 50 cikin ɗari na masu ɗauke da wannan cuta a faɗin duniya sun fitone daga Nijeriya, wanda kuma jihar Kano ta ɗauki kaso mai tsoka domin kuwa idan muka duba babban asibitin Murtala dake nan Kano, akwai kimanin masu ɗauka da wannan lalaura ta Sikila kimanin yara Dubu 10”.

Ta kuma ce ta hanyar gwaji ne kawai za a kaucewa ci gaba da samun yaɗuwar cutar ta Sikila.

Wani matashi kenanyayin da ake ɗaukar jikininsa

”Ya kamata masu niyyar yin aure su ƙara himma wajen sanin ajin jininsu kafin aure”

A tattaunawar sa da Labarai24 a madadin babban likitan da ke kula da sashen Farfesa Auwal Umar Gajida, shugaban kwamitin bada shawarwari na Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano, ya bayyana irin ƙalubalen da wannan sashe ya ke fusakanta na rashin isassun mutanen da su ke bada sadakar jini ”mu anan bamu san cewa idan kaje ka bada jini kamar ka bada sadaka ne kuma ita ma babbar sadaka ce.

”to sai dai za a iya cewa a yanzu mun fara samun ci gaba domin mutane da kansu yanzu suna zuwa domin kawo gudunmawar jini don taimakawa mabuƙata”.

Kimanin ɗalibai daga manyan makarantu daban daban ne a faɗin jihar nanne su ka halarci taron gangamin wanda aka gabatar a kwalejin ilimi ta Sa’adatu Rimi, dake nan Kano, tare da yi musu gwanjin jini kyauta.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan