Tsakanin Audu Bulama Bukarti da Gardi Zahra Mansur: Darasi da nazari da izina

  314

  Wato da farko dai ya kamata shi Bulama Bukarti ya godewa Allah. Mutane da yawa har da ni mai rubutun nan, mun kyautata masa zaton cewa shi ba mutumin banza ba ne, musamman da har za a zarge shi da harka da mata. Kuma wannan shaidar da ya samu daga bakuna masu yawa, tana da muhimmanci sosai, duk da cewa, ko me za a yi wasu ba za su yarda ba. Amma abin tambaya a nan, me ye in ka munana zato ga ɗan’uwanka, bayan abin da kake zaton, ba tabbas gare ka a kai ba?

  Wannan batu dole ne ya ɗaga hankalin mutane. Ba don komai ba sai don kasancewa shi Bukarti a kan gaba wajen tsage gaskiya da kuma bibiyar maha’inta. Da a ce wani karabutin ne aka same shi da wannan, to wataƙila da yanzu ba wannan labarin ake yi ba. Wataƙila da tuni ko kyautata masa zaton ma ba za a yi ba.

  To sai dai inda gizo yake saƙa shi ne, ya kamata Bukarti da ire-irensa da mu kanmu, duk mu ɗauki izina daga wannan dambarwa. Gaskiya ne, Bukarti mutumin kirki ne, kuma ɗan gwagwarmaya. To amma a sanina da shi a Fesbuk, ba kasafai ya fiye kula kowa ba. Da ma wasu daga sun ga sun sami followers da tarin likes, sai su zama wasu manyan ‘yan girman kai! Su ga intalaktuwals, ba za su dinga kula ordinary bloody common facebook ciɓilians ba. Duk da cewa zama shahararre “popular” a ko’ina yana da nasa ƙalubalen, domin ko mu da ba mu da mabin dubu 30 kamar gardi Zahra, za ka ga ba komai kake da lokacin yin “responding” ba, dole sai dai kana yi kana wuce wasu. To amma duk da haka, akwai waɗanda, ba ka fi su komai ba, ba ka fi su duk wani abu da kake tunani ba, ko ilimi ko shekaru ko shahara ko fitsara ko ma meye! To amma a gaskiya ni dai na sha nuna gamsuwata da lamuran Bukarti, amma ban taɓa ganin ya kula wani abu nawa ba. Amma fa na yi masa uzuri! Shi Celebrity ne, kuma ba shi da lokaci sosai, to amma a ina ya sami lokacin gardi Zahra?

  A ganina, babban abin da ya sa lamarin Bukarti ya bayar da wannan mamakin, saboda cewa an yarda mutumin kirki ne. Kuma wannan kawai ya ishe shi abin alfahari, duk da haka kuma, ya kamata a ƙara taka-tsantsan!

  Ba na son in yi wata warwara game da abin da Bulama Bukarti ya faɗa, domin ni na amince, saboda yadda nake kyautata masa zato, amma tuni na ga wasu suna ta “analysis” ɗin maganar. To amma ta inda a nan ma nake yi wa Bukartin uzuri shi ne, kuɗin an bayar da su ne, ba wai in a “formal way” ba, kuma ya tabbatar da cewa ba ma shi ya tura kuɗin ba. Ka ga wannan ya ishi duk wani mai taraddadi game da batun. Kuma ko su ‘yan sandan, in dai za su yi masa adalci, to a gaskiya bai kamata ma su dinga kaurara abin yadda suka yi ba.

  Me ya sa Bukarti ya yi sauri ya magantu – barazana (Blackmail)?

  Wasu suna ganin bai kamata Bukarti ya yi magana ba. To amma ya zama dole a kansa ya yi magana, domin akwai wani abu wanda da ya faru, da sai abin ya fi zame masa matsala. Maganar kuwa ita ce, a matsayin Bukarti na wanda ya fiye takurawa maha’inta, musamman ma kuma tun da akwai su a cikin ‘yan sanda, to tun lokacin da na ji Kiyawa yana nanata cewa “ai in aka ga sunayen waɗanda gardi Zahra ya cuta, za a sha mamaki”, to gara da ya yi zumbur ya ce wani abu. Amma da ya bari sai da ‘yan sanda suka gani sannan suka yi magana, lallai da abin ya fi rincaɓewa Bukarti.

  ‘Yan jarida, musamman irin su Nasiru Zango, sun yi wa Bukarti kara, don ban ji wannan zazzaƙan sautin nasa yana tashi a In Da Ranka ba, yau da wani ne, da tuni ka ji wannnnnnnnni babbbbbban abinnnnn ashhhhhhhhha yaaaaaaaaaaaaaaa…. Sai Allah Ya kiyaye, daga wajen abokinsa ne. Haka ma sauran wasu ‘yan jaridar, duk sun yi gum, domin dai ganin ƙimar shi Malam Bukartin.

  Ita Zahran gaskiyar: Bayan da aka nuno ta a gaske, a wajen ‘yan sanda, to a nan duk irin garada masu kwalamar son mata, ya kamata su mayar da kwalamarsu, domin abin da ya bayyana a gaske, ba daidai yake da abubuwan da ake mannawa a shafukan nata ba. Me nake so in ce? Hotunan nata da take sakawa a soshiyal midiya, sam, ba ta yi kama da su ba, ma’ana an yi amfani da kyamara an kara hoda da jambaki da kuma wani karin rashin kunyar. Don haka, matasa sai a kiyaye! Ba duk hotunan soshiyal midiya ba ne suke gaske, ana hadawa da a-cuci-garada.

  Shi gardin gasken, wato Musa L: a gaskiya ba ƙaramin zaƙwaƙurin tantirin shaixanin yaro ba ne wannan. Ya kamata hukuma ta hukunta shi, amma kuma ya yi qoqari wajen wankar garorin da suke ganin sun waye. Sau da yawa za ka ga mutum ya zo yana maka “analysis” raurau a Fesbuk, in ka yi magana ba ma ka ishe shi kallo ba, amma sai ya je can, abin kunya, ka ga yana yi wa wasu ‘yan yara sa’annin ‘ya’yansa ladabi da wasa da likes da duk wasu abubuwa da bai kamata a ce an ga sunansa a wajen ba. Wani lokacin, ni yarinyar da na sani a rayuwa ta haqiqa ma, in na ga ba ta da kamun-kai, ko kuma na ga ta yi wata shiririta mai girma, kuma in Musulma ce, nakan ji nauyin kula irin wannan. Ban ce ba na kulawa ba fa, kar wani ya je ya xauko shafina, amma dai gara a dinga sara ana duban bakin gatari, ya ku intalakcuwals.

  ZahraLeaks: su yanzu a Turai, har ma da wasu sassa na duniya, Wikileaks ne ya takura musu. Wani shafi ne mai kawo kwazozoton abubuwan da ake jin an yi su a cikin sirri, wanda Julian Assange yake jagoranta. To mu kuma ga shi yanzu mun samu ZahraLeaks, ko GardiLeaks, ko kuma ƊansittiLeaks, ko ma mu ce MusaLeaks, domin nan gaba kuma ba a san dubun su waye za ta fito daga cikin wannan Leaks ɗin ba. Har ma gara Bukarti, shi ya fitar da kansa, ya rage na mai yarda ya yarda, wanda kuma ba zai yarda ba, ya yi duk abin da zai yi.

  Wani abu dai da zai zame mana darasi a wannan dambarwar shi ne, ya kamata mu zama masu taka-tsantsan a cikin dukkanin lamuranmu.

  Allah Ya kiyaye mu, Allah Ya sa Bukarti ya fita daga wannan ibtila’in na soshiyal midiya lafiya, Allah kuma Ya sa Ya gane kuskurensa wanda na ambata a nan – a iya ɗan ƙaramin sanina – na share mutane. Gabaɗayanmu, Allah Ya yafe mana zunubanmu, Ya suturta aibukanmu, Ya raba mu da zamewa a duniya da lahira, amin!

  Muhammad Sulaiman Abdullahi malami ne a jami’ar Bayero ya rubuto daga Kano Najeriya

  Turawa Abokai

  RUBUTA AMSA

  Rubuta ra'ayinka
  Rubuta Sunanka a nan