Shugaban ƙasa Buhari zai bar Nijeriya zuwa ƙasar Rwanda

95

Shugaban ƙasa Muhammad Buhari, zai tashi daga Nijeriya zuwa ƙasar Rwanda, a yau Laraba, domin halastar taron ƙasashen rainon Ingila na Commonwealth karo na 20 da akayiwa laƙabi da CHOGM 2022.

Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasa na musamman kan kafafen sadarwa Femi Adesina, ya fitar ya bayyana cewa taron ƙasashen zai gudana daga ranar 20 zuwa 26 na watan Yuni,2022 inda zai maida hankali wajen ci gaba da tallafawa kimanin mutane sama da miliyan 2 da ke cikin ƙunshin ƙasashen.

Adesina ya kuma bayyana cewa a yayin taron shugaba Buhari, zai gabatar da jawabinsa kan samun karuwar cutar Maleriya da sauran cututtika da suka shafi ƙasashen.

Ka zalika ana saran shugaban zai tattauna da sauran shugabannin ƙasashen da su ka halarci taron.

Shugabannin ƙasashen zasu maida hankali kan muhimman abubuwan da su ka shafi hanyoyin farfaɗo da tattalin arziƙi duniya bayan da aka sha fama da cutar Korona, matsalar ɗumamar yanayi da tattauan hanyoyin rage talauchi, kasuwanci da inganta tsaro da dai sauransu.

Haka kuma shugaban ya samu rakiyar ministoci da sauran masu taimakawa shugaban na musamman.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan