Budurwa ta yi awon gaba da motar saurayinta a Kano a lokacin da ya fita sayen Shawarma

710

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta tabbatar da kama wata budurwa mai suna Ilham Kabir Ƙaraye da ake zarginta da sace motar saurayinta bayan da ya fita sayo musu Shawarma.

Kakakin rundunar ƴan sandan na Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya tabbatar da haka ga manema labarai a yau Litinin.

Kiyawa ya ce a ranar 12 ga Yuli, 2022 wani saurayi da ba a bayyana sunansa ba ya shigar da ƙorafi ga hukumar ƴan sandan jihar Kano kan sace masa mota.

Ya ƙara da cewa saurayin ya fita da budurwarsa zuwa yawon shaƙatawa a inda suka tsaya a daidai unguwar Ƙofar Famfo da ke birnin na Kano, domin ya sayo musu Shawarma wanda fitar sa ke da wuyar budurwar ta kira wani saurayinta suka tsere da motar.

A ƙarshe SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce za su gurfanar da wannan matashiya a gaban Shari’a da zarar sun kammala bincike.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan