Ba Na Garkuwa Da Mutane, Kashe Su Kawai Nake Yi — Aleru

340

Ƙasurgumin ɗan ta’addar nan, Ada Aleru, wanda kwanan aka naɗa shi sarautar Sarkin Fulanin Yandoton Daji, ya ce shi fa ba ya yin garkuwa da mutane, kashe su yake yi.

Bikin naɗin sarautar Aleru, wanda shi ne jagoran ‘yan ta’adda a ƙaramar hukumar Tsafe dake jihar Zamfara da ƙaramar hukumar Faskari ta jihar Katsina, ya jawo ka-ce-na-ce a faɗin Najeriya.

Bayan naɗin Aleru wannan sarauta, gwamnatin jihar Zamfara ta sauke Sarkin ‘Yandoton Daji, Aliyu Marafa.

Ana dai neman Aleru ruwa a jallo a jihohin Katsina sakamakon yadda yake kashe mutane ba ji ba gani.

Gwamnatin jihar Katsina dai ta ce za ta bada tukwicin naira miliyan N5 ga duk mutumin da ya bada bayanin inda Aleru yake.

Aleru ya taɓa kashe mutum 52 a Kadisau, wani ƙauye da yake cikin Faskari a 2019.

A tattaunawarsa ta farko da BBC, Aleru ya ce shi fa yana jin haushin Hausawa da gwamnatin Najeriya.

A wani shiri da BBC za ta watsa ranar 25 ga Yuli, 2022, Aleru ya ce yayin da yaransa suke garkuwa da mutane, shi kashewa kawai yake yi, kamar yadda jaridar Premium Times ta rawaito.

“Yarana suke yin haka, ni kashewa kawai nake yi”, in ji Aleru.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan