ASUU Ta Ƙara Mako 4 A Yajin Da Take Yi

188

Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya, ASUU, ta ƙara mako huɗu a yajin aikin da take ci gaba da yi.

Shugaban ASUU na ƙasa, Farfesa Emmanuel Osodeke ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin.

Ya ce Kwamitin Zartarwa na Ƙasa na ASUU, NEC, ne ya ɗauki wannan mataki bayan wani taron tattaunawa da suka yi game da gazawar gwamnati na cika alƙawuran da take yi wa ƙungiyar.

A ranar 9 ga Fabrairu, 2022 ne ASUU ta fara yajin aikin sai-baba-ta-gani da nufin tilasta wa Gwamnatin Tarayya biya mata buƙatunta.

Zuwa yanzu ƙungiyar ta shafe kwanaki 173 tana wannan yajin aiki.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan