Yajin Aikin ASUU: Wanne hali ɗaliban jami’a su ke ciki a Najeriya?

168

A tsakiyar watan Fabarairu shekarar nan ne kungiyar malaman jami’o’i ta Najeriya, ASUU, ta tsunduma yajin aiki sakamakon abin da ta bayyana a matsayin gazawar gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari wajen aiwatar da jarjejeniyar da suka kulla a baya game da yadda za a inganta harkokin karatun jami’a na ƙasar nan.

Rahotanni sun nuna cewa kungiyar ta ASUU ta shiga yajin aiki sau 15 tun bayan dawowar mulkin dimokuradiyya Najeriya cikin shekarar 1999, lamarin da kan jefa harkokin karatu cikin mawuyacin hali.

Haka kuma Yajin Aikin ya fi yin tasiri a kan dalibai wadanda ke tsintar kansu cikin damuwa, dalilin da ya sa wasu ke shiga wasu abubuwan musamman sana’o’in dogaro da kai a maimakon zama a gida.

Wanne hali ɗalibai su ke ciki?

A tattaunawar da Labarai24 ta yi da wasu daga cikin ɗaliban jami’o’in Najeriya, wasu daga cikinsu sun bayyana cewa tuni su ka rungumi ƙananan sana’o’i domin sun yanke ƙauna da tsarin karatun jami’o’in gwamnati a ƙasar wasu kuma sun yanke ƙauna daga karatun boko kwata – kwata.

Fatima Muhammad ɗaliba ce a jami’ar Yusuf Maitama Sule da ke birnin Kano ta bayyana cewa bayan da ƙungiyar ASUU din ta shiga Yajin Aikin tuni ta rungumi harkokin kasuwanci tare da shiga shafukan da su ke bayar da horo na musamman akan harkokin sana’a kyauta a shafukan intanet.

Alhamdulillah. Bayan ƙungiyar ASUU sun tafi Yajin Aiku, na yi ƙoƙarin ganin na mayar da hankalina wajen karatun addini, sannan na mai da hankali wajen kasuwancin da na ke yi wanda a lokacin da muke makaranta bakomai nake samun yi ba”

Haka kuma na halarci Online Classes da yawa gaskiya kamar Learning Skills and Products Management wanda kungiyar Ingressive for Good ta ɗauki nauyi. Bayan haka na shiga practical class da ake koyar da girki domin amfanin kaina.”

Shi kuwa Mustapha Sani Mudi da ke karatu a jami’ar Bayero cewa ya yi tuni ya rungumi sana’ar noma kasancewar sa mutumin karkara ya kuma yi fatan gwamnati da kungiyar ASUU za su cimma daidaito domin komawa bakin aiki .

“Ina fatan su dawo domin mu ƙarasa karatunmu. Kuma a halin yanzu kasancewata mutumin karkara na rungumi harkar noma a maimakon in yi ta zama haka. Kuma lallai wannan Yajin Aikin ya ƙara tabbatar min da cewa karatun Boko ba komai ba ne a ƙasar nan”

Ita kuwa Lailah Muhammad Bawa da ke karatu a jami’ar kimiyya da fasaha da ke garin Wudil, cewa ta yi tuni ta fidda rai daga karatun boko la’akari da yadda gwamnatin tarayya ta yi wa ɓangaren riƙon sakainar kashi.

Tun fara Yajin Aikin ƙungiyar ASUU ba na aikin komai zaman gida kawai na ke yi, kuma tuni na cire rai akan Karatun boko a halin yanzu. Amma idan Allah ya yi zan cigaba da karatun boko to Alhamdulillah. Amma gaskiya na cire rai sai yadda Allah ya yi damu.”

Alal haƙiƙa na dawo gida ina aiki a gidan gonar ɗan uwan mahaifina, Babuba Integrated Farms da ke jihar Kaduna.
Jerin yajin aiki da ake maimaitawa a lokacin da na ke karatu yasa na gane cewa karatu a makarantun gwamnatin a Najeriya ɓata lokaci ne da takaici.

A halin yanzu mun cire rai da wannan gwamnatin watakila komawa sai sabuwar gwamnati” In ji Mubarak Ahmad dalibi a jami’ar Yusuf Maitama Sule.

Ita ma Aisha Ibrahim Jibril wacce ta kasance ɗaliba kuma ta ke gudanar da ƙananan sana’o’i a cikin jami’a, yanke ƙauna ta yi daga tsarin karatun jami’o’in la’akari da yadda lamarin ya shafe ta a ɓangare biyu.

“A matsayina na ɗaliba wacce ta ke da burin yin aure bayan na kammala karatuna wannan yajin aikin ya dakatar da ni da kuma kasuwancin da na ke yi saboda a makarata na ke yi, sannan wannan yajin aiki ya sa ina ji a raina cewa karatun Boko ba shi da wani amfani a wannan ƙasar.”

Malaman jami’o’in gwamnati Najeriya da sauran wasu ƙungiyoyin ma’aikata a bangaren ilimi na yajin aiki sama da watanni biyar saboda gazawar gwamati wajen cika alƙawarin yarjejeniyar da ta yi da ƙungiyoyin.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan