‘Yan Najeriya Sun Kashe Tiriliyan N1.25 Akan Kiran Waya Da Data A 2022

269

Ma’abota amfani da wayar hannu a Najeriya sun kashe kimanin tiriliyan 1.25 akan kiran waya da data a watannin shidan farko na 2022.

Wannan na ƙunshe ne a cikin wani rahoton kuɗi na rabin shekara da MTN Nigeria da Airtel Africa suka fitar.

Wannan adadi ya ƙaru da kaso 17.77 cikin 100 na adadin kuɗaɗen da kamfanonin biyu suka samu a 2021.

A watanni shida na farkon 2022, MTN Nigeria ta samu biliyan N850.33 tsakanin kira da data, ƙarin biliyan N717.56 da ta samu a 2021.

Airtel ya bayyana cewa ya samu biliyan N399.39 daga kira da data, ƙarin biliyan N343.63 da ya samu a 2021.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan