Joshua Dariye Ya Samu Tikitin Takarar Sanata A Jam’iyyar Labour

253


Tsohon Gwamnan jihar Filato, Joshua Dariye, zai yi takarar sanata a Mazabar Sanata ta Filato ta Tsakiya a ƙarƙashin tutar jam’iyyar LP bayan samun sa da laifin sace naira biliyan N1.126 da Kotun Ƙoli ta yi.

A ranar Litinin ne aka saki Mista Dariye, Jolly Nyame, da wasu mutum uku bayan Shugaba Muhammadu Buhari ya yafe musu satar kuɗaɗen da suka yi.

A ranar 14 ga Afrilu, 2022 ne Shugaba Buhari ya yafe wa mutanen bayan wani taron Majalisar Tsaro ta Ƙasa.

Dariye, wanda aka yanke wa hukuncin zaman gidan yari na shekara 10, sakamakon satar naira biliyan N1.126, an sake shi ne bayan ya shafe shekara huɗu a gidan yari.

Wasu sahihan majiyoyi sun tabbatar da jaridar Daily Trust cewa jam’iyyar LP a jihar Filato ta gama shirye-shiryen karɓar Dariye don ya yi mata takarar sanata.

Dariye dai ya yi Gwamnan Filato ne a PDP, inda daga bisani ya sheƙa zuwa LP, ya yi takarar sanata kuma ya ci a 2011.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan