Yadda Wani Ɗan China Ya Hallaka Tsohuwar Budurwarsa A Kano

128

Wani ɗan ƙasar China mai suna Mr Geng, ya kashe masoyiyarsa ‘yar Najeriya mai Ummukulsum Buhari wadda suka daɗe suna soyayya.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wani gajeren labari da fitaccen ɗan jaridar nan mazaunin jihar Kano, Nasir Salisu Zango ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Asabar.

Mista Geng ya samu labarin Ummukulsum ta yi aure ne, abin da yasa ya kashe ta.

Ya kashe ta ne a gidanta dake Janbulo, a cikin ƙaramar hukumar Gwale, kuma aka kai ta Asibitin UMC inda rai ya yi halinsa.

Ummukulsum, wadda aka fi sani da Ummita, ta gama digirin farko a Fannin Aikin Gona a Jami’ar Kampala, Uganda, kuma kafin rasuwar ta tana bautar ƙasa ne a Sokoto

Jami’an hana fasa ƙwauri da ‘yan sanda ne suka ƙwace Mista Geng daga mutanen da suka fara sassama shi a unguwar ta Janbulo, kusa da Layin Lawan Kyankyan, kamar dai yadda Nasir Salisu Zango ya bayyana.

Yanzu haka yana hannun ‘yan sanda.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan