Gwamnatin Kano Ta Kama Mushen Dabbobi A Mayankar ‘Yan Awaki

40

Hukumar Kare Haƙƙin Masu Sayen Kayayyaki ta Jihar Kano, CPC, ta kama mushen dabbobi a mayankar ’Yan Awaki dake Unguwa Uku a ƙaramar hukumar Tarauni dake jihar.

Mai Magana da Yawun hukumar, Musbahu Yakasai ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa ga manema labarai ranar Talata, kamar yadda jaridar Aminiya ta rawaito.

A cewarsa, hukumar ta samu labarin dabbobin ne da misalin ƙarfe 6:00 na safiya.

Babban Mataimaki na Musamman ga Gwamnan Jihar Kano Kan Ingancin kayayyaki, Salisu Muhammad ne ya wakilci Shugaban Hukumar, Baffa Babba Dan’agundi a wajen kama dabbobin.

“Mun sami labari daga wasu mutane masu kishi cewa an kawo matattun dabbobi a mayankar da suka haɗa da raguna da awaki bayan an yanka su a wani waje.

“Nan take tawagarmu ta ɗauki mataki tare da kame dabbobin a ƙoƙarinmu na kare mutanen Kano daga amfani da kayayyaki na jabu da lalatattun kayayyaki”, in ji Musbabu.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan