Shin Da Gaske Ne Abba Gida Gida Ya Buƙaci A Taimaka Masa Da Kuɗin Kamfe?

47

Ɗan takarar gwamnan jihar Kano a jam’iyyar ANPP, Abba Kabir Yusuf da aka fi sani da Abba Gida Gida, ya nesanta kansa da yunƙurin tara masa kuɗaɗen yaƙin neman zaɓe da ake zargin wata ƙungiya mai suna ‘Abokan Abba Gida’ za ta yi.

Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Abba, Sanusi Dawakin Tofa, ya fitar ranar Talata a Kano.

Tun da farko dai wani bidiyo ne ya karaɗe shafukan sada zumunta da ya ce ɗan takarar gwamnan na NNPP yana buƙatar kowane ɗaya daga cikin magoya bayansa ya ba shi N1000 don yaƙin neman zaɓe.

Abba ya ce an jawo hankalinsa ga wani bidiyo da ya karaɗe ko’ina da yake cewa ya amince kowane ɗaya daga magoya bayansa ya ba shi N1000 a matsayin gudunmawa.

A cewar Abba Gida Gida, yana sane da bidiyon, ya kuma bayyana shi da wani yunƙuri na ‘yan adawa don ɓata masa suna da jam’iyyarsa ta NNPP.

Saboda haka ne Abba ya yi kira ga magoya bayansa da su yi watsi da bidiyon.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan