Ɗan China Da Ya Kashe Budurwarsa A Kano Ya Baƙunci Kotu

107

An gurfanar da Geng Quanrong, ɗan China da ya kashe tsohuwar budurwarsa a gaban wata Kotun Majistire a jihar Kano.

Idan dai za a iya tunawa, Mista Quanrong ya kashe budurwarsa mai suna Ummakulsum Sani Buhari da aka fi sani da Ummita ta hanyar amfani da wuƙa a unguwar Janbulo dake ƙaramar hukumar Gwale a jihar Kano.

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ce ta maka Mista Quanrong a kotun bisa zargin sa da laifin kisan kai, laifin da ya saɓa wa sashi na 221 na dokokin penal code.

Kotun ta bada umarnin a ci gaba da tsare shi har zuwa ranar 13 ga Oktoba, 2022.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan