Cin Hanci: An Yanke Wa Minista Hukuncin Kisa A China

64

An yanke wa Sun Lijun, tsohon Mataimakin Ministan Tsaron Jama’a na China hukuncin kisa sakamakon samun sa da laifin karɓar nagoro, yi wa kasuwar hannun jari zagon ƙasa da kuma mallakar makamai ba bisa ƙa’ida ba.

Ko a ranar Alhamis an yanke irin wannan hukunci ga wani tsohon jami’in gwamnati mai suna Fu Zhenghua sakamakon samun sa da laifin laƙume yuan miliyan 117 (daidai da dalar Amurka miliyan 16.76) da kuma laifin sauya doka don biyan buƙatar kansa.

Kotu ta kuma samu Mista Sun da laifin karɓar nagoro a muƙaman da ya riƙe daban-daban daga 2001 zuwa 2020.

An kuma hana Mista Sun shiga dukkan wasu harkokin siyasa har ƙarshen rayuwarsa, kuma an ƙwace duk kadarori da ya mallaka, kamar yadda Kotun Jama’a ta Changchun dake Lardin Jilin ta bayyana.

Kotun ta kuma tabbatar da cewa Mista Sun ya karɓi kuɗi da kadarori da darajarsu ta kai yuan miliyan 646 (daidai da dalar Amurka miliyan 92.39).

An kuma same shi da laifin yin maguɗi a kasuwar hannun jari a watanni ukun farko na 2018, inda ya taimaka wa wasu mutane suka guje wa yin asarar yuan miliyan 145.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan