Gabatar Da Kasafin Kudi: Ina son barin abin tarihi a Najeriya – Buhari

312

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya ce gwamnatinsa na son barin abin tarihi a kasar fiye da yadda ya same ta a 2015.

Buhari ya bayyana hakan ne a yayin da yake gabatar da daftarin kasafin kudin kasar na shekara mai zuwa 2023 ga gamayyar majalisun dokokin kasar yau a Abuja.

Kasafin kudin ya kunshi Naira tiriliyan 20.15, inda daga ciki gwamnatin za ta kashe tiriliyan 8.21 a harkokin yau da kullum kamar su albashi da sauransu da kuma naira tiriliyan 5.15 a manyan ayyuka.

Haka kuma a kasafin gwamnatin ta tsara kashe Naira tiriliyan 6.31 wajen biyan bashi.

Kasafin kudin ya ta’allaka ne a kan gangar mai miliyan 1.69 da kasar za ta rika hakowa kullum, tare da sayar da shi a kan Dala 70 kan kowa ce ganga, inda kuma Dala daya za ta kasance a kan Naira 435.

Wannan dai shi ne karo na takwas kuma na karshe da zai gabatar da kasafin kudin kafin barinsa mulki a shekara mai zuwa a wa’adinsa na biyu kuma na karshe.

A bayanan ya nuna cewa fannonin da gwamnatinsa za ta fi mayar da hankali a kasafin sun hada da aikin titi da layin-dogo (na jirgin kasa) da wutar-lantarki.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan