Murna ta koma ciki: Yajin aikin da muka janye na wucin gadi ne – ASUU

224

Ƙungiyar Malaman Jami’oin Najeriya, ASUU, ta ce yajin aiki na watanni takwas da ta janye a ranar Juma’a fa na wucin gadi ne.

A cewar ASUU, shugabannin ƙungiyar za su sake nazartar mataki na gaba da za su ɗauka musamman game da batun hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara da ya buƙaci su su koma aiki nan take ba tare da ɓata lokaci ba.

Ƙungiyar malaman jami’o’in Najeriya dai ta fara yajin aiki ne tun ranar 14 ga Fabrairu, 2022.

A safiyar yau Juma’a ne shugabannin ƙungiyar suka sanar da dakatar da yajin aikin sai dai bisa wasu sharuɗa da suka ce matuƙar ba a cim masu ba to kuwa ungulu za ta koma gidanta na tsamiya.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan