Wata taƙaddama tsakanin manoma da fulani ta yi sanadiyyar mutuwar wani magidanci a jihar Kano da ke arewacin Najeriya.
Rikicin wanda ya faru a kauyen Gotawa da ke yankin ƙaramar hukumar Gwarzo ya kuma yi sanadiyyar jikkatar mutum biyar.
Tun da farko manoman sun zargi makiyayan ne da shigar musu gona tare da lalata musu amfanin gonar da su ke tsaka da aiki akan su.
Rundunar yan sanda ta jihar Kano ta tabbatar da faruwar lamarin a ta bakin kakakinta SP Abdullahi Haruna Kiyawa, inda ya ƙara da cewa waɗanda su ka samu jikkatar na kwance a babban asibitin Gwarzo inda su ke karɓar magani.
SP Abdullahi Kiyawa, ya ce tuni jami’an ƴan sanda su ka fara bincike akan faruwar lamarin.
Idan za a iya tunawa dai a shekarar 2018 Gwamna Abdullahi Ganduje ya gayyaci Fulani makiyaya su koma jiharsa domin gudanar da kiyo ba tare da samun matsala ba.