Ba Zan Yi Kwankwaso Ba A Zaɓen Shugaban Ƙasa— Naja’atu

110

Fitacciyar ‘yar siyasar nan kuma ‘yar gwagwarmaya, Naja’atu Bala Mohammed, ta ce ba za ta zaɓi ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP, Rabi’u Musa Kwankwaso ba a zaɓen bana.

Naja’atu ta bayyana haka ne ranar Lahadi a yayin wata tattaunawarta da Freedom Radio, Kano.

A cewarta, za ta duba cancanta ne a kowane mataki.

“Abin da ya yi sa na fita daga jam’iyyar APC don ba zan sa kaina a cikin keji ba. Keji shi ne cewar duk jam’iyyun nan ba su da bambancin aƙida. Ga baki ɗayansu duk iri ɗaya ne, duk aƙidar iri ɗaya ce.

“Amma, ya kamata mu kalli jam’iyya a matsayin riga. Riga ce. Ka ga misali da, Buhari, ai a APP yake da, muka dawo muka koma ANPP. Daga ANPP ya yi tsallen baɗake ya shiga CPCnsa, ya dawo yanzu kuma ake APC.

“Amma Buharin nan ne dai. To kodayaushe ya ga dama, kodayaushe kowane ɗan siyasa ya ga dama zai sa rigar da yake so”, in ji Naja’atu.

“Haka zalika Kwankwaso. Da yana PDP, ya dawo ya yi APC, ya koma PDP, yanzu yana NNPP. Amma Kwankwason nan ne dai. Haka Atikun.

“To maganar da muke faɗa shi ne, a yanzu da muke kan gaɓa, hauka ne mu ce za mu bi riga ba mutum ba. Shi ya sa ni na fara wannan ƙundumbalar na fita daga cikin jam’iyyar APC.

“A yau ba sai gobe ba, ina tare da Binani, ‘yar takarar gwamnan APC da take Adamawa. A gobe zan tafi Adamawa in je in yi mata kamfen.

“A Kano zan zo in yi wa Abba Gida Gida kamfen, a NNPP”, in ji ta.

“A sama zan yi wa Atiku kamfen, saboda na duba ‘yan takarkarun duka, na auna su. In da son samu ne da na yi Kwankwaso amma ba shi da karɓuwa. Ba kuma zai iya samun karɓuwa akan wannan ɗan ƙalilan lokaci ba.

“To saboda haka shi ya sa na fita daga APC. Kuma ba zai yiwu in zauna a cikin APC, in zo ina yi mata antifati ba, doka ta hana a yi haka. Saboda haka na fita. Shi ne magana”, ta ƙara da haka.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan