Sauya Kuɗi: Ana Ƙoƙarin Sasantawa Tsakanin Gwamnatin Tarayya Da Gwamnoni

155

Wasu alamu na nuna cewa ana ƙoƙarin sasantawa tsakanin gwamnatin tarayya da gwamnonin da suka kai Babban Bankin Najeriya, CBN, ƙara game da manufar sauya kuɗi, kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito.

Idan dai ba a manta ba, jihohin Kaduna, Kogi da Zamfara ne suka fara garzayawa Kotun Ƙoli inda suka roƙe ta ta hana CBN aiwatar da manufar sauya takardun kuɗi na N200, N500 da N1000 daga 10 ga Fabrairu, 2023.

Haka ma, jihohin Kano, Bayelsa da Edo sun bi sahun jihohin da suka maka CBN a Kotun Ƙolin.

A zaman kotun na ranar Laraba, 15 ga Fabrairu, Kotun Ƙoli ta ɗage sauraron ƙarar zuwa 22 ga Fabrairu, 2022.

Sai dai a jiya da daddare gwamnatin tarayya ta tuntuɓi wasu jihohin da suka kai ƙarar da nufin sasantawa a wajen kotu.

Gwamnatin jihar Kaduna, a cikin wata sanarwa da ta fitar a jiya da daddare ta ce wasu jami’an gwamnatin tarayya sun tuntuɓi Gwamna Nasir El-Rufai da wasu gwamnonin da nufin sasantawa.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan