Hotuna: Yadda Sojoji su ka Cafke Wasu Matasa da ke Yinƙurin Ƙone Ofishin Zaɓe a Rano

272A yayin da ake tsaka da karɓar sakamakon zaɓe na mazaɓu 10 a ƙaramar hukumar Rano, wasu matasa ɗauke da makamai sun shiga hannu jami’an soji bayan da su kayi yin ƙurin kuzawa cikin ofishin INEC.

Matasan wanda shekarunsu basu gaza 30 ba sun shiga hannun hukumar soji bayan da su kayi yin ƙurin shiga wurin da ake tattawa da faɗar sakamakon zaɓe na gwamnoni da ‘yan majalisun jiha wanda ya gudana a jiya Asabar.

Tuni dai aka miƙa waɗannan ɓatagarin zuwa hannun jami’an ‘yan sanda don ci gaba da gudanar da bincike.

Kafin wannan lokacin dai a yammacin ranar Asabar 18 ga Maris, 2023 sai da aka zargi wasu mutane da shigowa da wata mota mai ɗauke da lambar ƙaramar hukuma ɗauke da makamai wanda har sai da takai da Hukumar tsaro ta farin kaya ta harbi ɗaya dana cikin ɓatagarin a ƙafa.

Matasan dai na ɗauke da mugwgwan makamai da su ka haɗa da wuƙaƙe, barandami harma da makamashi na man fetur wanda ake zargin sunzo da nufin ƙone ofishin na INEC.

Nan gaba kaɗan zaku jimu da kakin rundunar ‘yan sanda donjin mataki na gaba.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan