Doguwa ya janye daga takarar shugaban majalisar wakilai , ya goyi bayan Abbas.

130

Alhassan Ado Doguwa, shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai ya janye daga takarar shugaban majalisar.

Doguwa ya bayyana janyewarsa daga takarar ne a daren Laraba a wani taro da aka yi da sababbin zababbun yan majalisar wakilai a otal din Transcorp Hilton da ke Abuja.

Haka ma Abubakar Maki da Olatunji Olawuyi suma sun janye daga takarar.

Femi Gbajabiamila, kakakin majalisar; Tajudeen Abbas da Benjamin Kalu sun halarci wajen taron.

Doguwa ya ce ya janye burinsa na zama kakakin majalisar ne tun ranar da jam’iyyar APC ta tsayar da Abbas da Kalu a matsayin wadanda za su yi mata kakakin majalisar wakilai da mataimaki.

Doguwa ya ce Abbas ya cancanta kuma yana da gogewar aikin majalisar da zai iya jagorantar ’yan majalisun su 359.

Ya ce ya janye daga takarar ne domin ya goyi bayan zabin jam’iyyar saboda shi ma ya ci gajiyar tsarin rabon shiyya-shiyya.

Fitowar Doguwa takarar shugancin kakakin majalisa ta 10th da kuma janyewar tasa daga neman kujerar ya ba wa mutane da yawa mamaki domin.

An alakanta Doguwa da G7 – kungiyar yan bakwai masu neman takarar shugaban kakakin majalisar kasa – wadanda suka sha alwashin cewa dole sai dai a zabi kakakin majalisar wakilai na 10 daga cikinsu.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan